An rufe makarantu 22 bayan korona ta yadu tsakanin dalibai

An rufe makarantu 22 bayan korona ta yadu tsakanin dalibai

Ministan Ilimi na ƙasar Faransa, Jean-Michel Blanquer, a ranar Juma'a ya tabbatar da rufe makarantu 22 saboda ƙaruwar cutar coronavirus.

Mista Blanquer ya ce fiye da rabin sabbin wadanda suka kamu da cutar sun fito ne daga La Reunion.

Da ya ke zanta wa da gidan rediyon Europa 1, ya ce ya gamsu da yadda lamura ke tafiya tun bayan da dalibai suka koma makaranta ranar Talata.

An rufe makarantu 10 a cikin birnin Faransa yayin da sauran 12 kuma daga wani yanki ne na La Reunion inda ake samun sabbin wadanda suka kamu.

An dakatar da ajujuwa kimanin 130 a makarantun kuma ministan ya ce mahukunta suna bincike a kan sabbin mutum kimanin 250 da ke kamuwa da cutar ta sanadin makarantu a kullum.

Mutanen suna kamuwa da cutar ne daga wasu mutanen a wajen makaranta da ya yi wu sun kamu tun watanni da suka gabata.

A kan rufe makarantun idan an samu fiye da mutum uku da suka kamu da ƙwayar cutar ta Covid-19.

An rufe makarantu 22 bayan korona ta yadu tsakanin dalibai
An rufe makarantu 22 bayan korona ta yadu tsakanin dalibai
Source: UGC

DUBA WANNAN: Bidiyo: An kama wani dumu-dumu yana ƙoƙarin yin zina da matar mai gidansa

A halin yanzu ana samun hauhawar sabbin wadanda ke kamuwa da cutar a Faransa inda aka samu mutum 7,157 da suka kamu a ranar Alhamis.

A wani labari na daban, Gwamnatin Tarayyar Najeriya a ranar Juma'a ta karbi samfurin rigakafin cutar korona na ƙasar Rasha.

Jakadan Rasha a Najeriya, Alexey Shebarshin ne ya mika wa ministan lafiyar Najeriya, Osagie Ehanire rigakafin yayin ziyarar da ya kai ma'aikatar lafiyar a Abuja.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ma'aikatar, Olujimi Oyetomi.

An yi wa sanarwar laƙabin da 'Jakadan Rasha a Najeriya, Alexey L. Shebarshin ya kawo rigakafin COVID-19 na Rasha yayin ziyarar da ya kai wa ministan lafiyar Najeriya.'

A baya, The Punch ta ruwaito cewa shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasarsa ta amince da wani rigakafi da ke bayar da kariya daga coronavirus.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, daga baya ta ce za ta yi nazarin ingancin rigakafin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel