Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano

Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano

Ƙaramin yaro Ismail Yusuf ya ɗauki hoto a gaban sabon shagonsa da ya yi wa laƙabi da 'Rano shopping complex' a garin Rabo a jihar Kano.

A gano cewa ƴan Najeriya ne suka tallafawa yaron da jari da kayan masarufi ya buɗe shagon bayan hotonsa yana sayar da maggi cikin katan ya basu dandalin sada zumunta.

Yaron ɗan makarantar frimare ya ɗauki hotuna a gaban 'kantinsa' a Kano.

Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano
Hoton Ismail na farko da ya fara daukan hankalin mutane suka tallafa masa da kudi don bude babban shago
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa yana da ra'ayin fara kasuwa domin ya taimaka wa ƴan gidansu.

Ga dai hotunan a ƙasa:

Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano
Hoton sabuwar babban shagon da yaro Ismail ya bude a Rano, Kano.
Asali: Twitter

Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano
Ismail a cikin sabon shagonsa a garin Rano da ke Kano
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matashi mara aikin yi ya samu kyautar sabuwar mota saboda riko da gaskiya

Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano
Ismail sabon dan kasuwa na gyara kaya a cikin sabon shagonsa da ke Rano a Kano
Asali: Facebook

A wani labarin daban, wani matashi Abba Ahmad ya haƙura da shirin da ya yi na kashe kansa sakamakon rashin samun damar auren ɗiyar Shugaba Muhammadu Buhari, Hanan Buhari.

Ahmad ya haƙura ne bayan shawarwari da jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya suka bashi kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ahmad, ɗalibin jami'ar Maitama Sule ta Kano (tsohuwar jami'ar North West) ya daɗe yana aika sakon neman Hanan ta aure shi a Facebook da Instagram.

Matashin da mahaifinsa ya rasu tun a shekarar 2013 ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa kyawun Hanan da karatun da ta yi ne ya ke burge shi.

Hanan, mai shekaru 22 ta yi karatu ne a fanin koyon ɗaukan hoto a Jami'ar Ravensbourne da ke Ingila.

"Ina ƙaunar Hanan ne saboda kyawun fuskarta, karatun boko da ta yi da kuma gaskiya irin na mahaifinta (Shugaba Buhari).

"Na yi ƙoƙarin sanar da ita amma ban san ko saƙon ya isa wurin ta ba," in ji Ahmad.

Ya rubuta a shafinsa cewa zai kashe kansa idan Hanan ta auri wani namiji daban a ranar Juma'a.

A lokacin da majiyar Legit.ng ta tambayi dalilin da yasa zai kashe kansa saboda mace, ya ce: "Na faɗa ne kawai."

Kakakin rundunar ƴan sandan Kano, Abdullahi Haruna ya ce bisa umurnin Frank Mba ya gayyaci Ahmad zuwa hedkwatar su inda aka bashi shawarar kada ya kashe kansa.

Kwamishinan ƴan sanda Habu Sani da limamin ƴan sanda duk sun bashi shawarwari.

Kakakin rundunar ƴan sanda na ƙasa, Frank Mba ya yi magana da Ahmad a wayar tarho na tsawon minti 6 da daƙika 6 inda ya bashi shawarar kada ya kashe kansa duk da bai auri yar shugaban ƙasa ba.

An tunatar da shi cewa zai iya auren wata matar ƙyayawa kuma addinin sa ya hana mutum ya kashe kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel