Dalilai 5 da ya sa zan cigaba da zama a Barcelona - Lionel Messi

Dalilai 5 da ya sa zan cigaba da zama a Barcelona - Lionel Messi

- Daga karshe Lionel Messi ya amince da cigaba da zama a Barcelona bayan makonni biyu ana tafka muhawara

- Dan kwallon ya ce iyalansa sun nuna basu son barin kungiyar kwallon

Lionel Messi wanda ya yanke shawarar cigaba da zama a kungiyar kwallon Barcelona ya bayyana dalilan da yasa ya hakura kawai zai cigaba da taka leda a Cataloniya.

Dan shekara 33 wanda ya bayyanawa shugabannin kungiyar niyyar tafiya bayan shan kashin da suka fuskanta saura kiris ya tsallaka Ingila ya bugawa Manchester City.

Ya amince da cigaba da zama a Barcelona zuwa karshen kakar 2020/2021.

Ga dalilai biyar da ya bada na cigaba da zama:

1. Na yi tunanin zan iya tafiya ne. Shugaban kungiyar ya ce yanzu zan iya tafiya karshen kakar nan.

2. Zan cigaba da zama saboda shugaban ya fada min cewa wajibi ne in biya €700m idan ina son tafiya kuma hakan ba zai yiwu ba

3. Sun kafa hujjar cewa ban bayyana niyyar tafiya ba tun a watan Yuni

4. Mafita daya shine kuma in kai su kotu, amma ba zan taba kai Barcelona kotu ba saboda ina son kungiyar, ita ta bani komai lokacin da na zo

5. Lokacin da na fadawa uwargidata da yarana cewa zan tafi, sai da mukayi gajeruwar rikici. Dukkansu suka fara kuka, yaran ba su son barin Barcelona, kuma ba su son a canza musu makaranta

Dalilai 5 da ya sa zan cigaba da zama a Barcelona - Lionel Messi
Dalilai 5 da ya sa zan cigaba da zama a Barcelona - Lionel Messi
Source: Depositphotos

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel