Hotunan kanin gwamna ya na asuwaki da cinyar kaji sun jawo cece-kuce
A wani hoto da ke yawo a dandalin sada zumunta an ga Frank Ayade, dan uwa wurin gwamnan jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade, da manyan kwanukan naman kaji a gabansa yana kalaci dasu.
Wasu daga cikin ma'abota dandalin sada zumunta da suka yada hotunan sun kira Frank da ''mataimakin gwamna'' wasu kuma da ''gwamna na biyu''.
A wani takaitaccen sako da Faruk Adejoh-Audu ya wallafa dauke da hotunan Frank a shafinsa na Facebook, ya rubuta cewa: "Frank Ayade, kani kuma na hannun damar gwamna Ayade da ake kira ''mataimakin gwamna'' a jihar Kuros Riba kenan yayin da ya ke cin abincinsa.
Gwamnatin jihar Kuros Riba ta taba tsare wani dan jarida mai suna Agba Jalingo saboda wallafa wani rahoto da ya soki kanin gwamnan a shekarar 2019.
"Gwamna na biyu kenan a jihar Kuros Riba, Frank Ayade, yayin da ya ke shakatawa. A tafa masa," kamar yadda Jalingo ya rubuta.
Shi kuwa Silas Rimdans, wani ma'abocin amfani da dandalin Facebook, tambaya ya yi; "wannan abincin na kwana nawa ne yallabai?"
DUBA WANNAN: Tabarbarewar tattalin arziki: Sanusi ya bawa gwamnatin Buhari satar amsa a kan hanyar farfado da darajar Naira
Duk da babu wani karin bayani dangaen da wuri ko lokacin da aka dauki hoton, wasu daga cikin wadanda suka yi magana a kan hoton sun bayyana cewa an dauki hoton ne ranar 18 ga watan Agusta, yayin bikin murnar ranar zagayowar ranar haihuwar Frank.
Hotunan sun kara fusata wasu ma'abota dandalin sada zumunta saboda sun ci karo da su a daidai lokacin da jama'a ke gunaguni a kan halin kunci da tsadar rayuwa da suke ciki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng