Matashi mara aikin yi ya samu kyautar sabuwar mota saboda riko da gaskiya

Matashi mara aikin yi ya samu kyautar sabuwar mota saboda riko da gaskiya

Shugaban matasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, shiyar Kudu maso gabas, Olisaemeka Onyeka ya yi wa wani mazaunin Abuja Okocha Ifeanyichikwu kyautan mota saboda gaskiyarsa.

Ifeanyichikwu ya mayarwa Oscar Obi, babban masharwarci na musamman ga mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ovie Omo Agege wayarsa.

Onyeka ya ga labarin abinda ya faru tsakanin Obi da Ifeanyichikwu a dandalin sada zumunta kuma ya nemi lambar wayarsa ya kira shi.

Onyeka
Onyeka
Source: Twitter

Mashawarcin na musamman ya manta da wayarsa ne a motar Ifeanyichikwu a lokacin yana sauri ya tafi wani taro a ranar 30 ga watan Agusta.

Onyeka ya kira Ifeanyichikwu ya masa godiya sannan daga baya ya masa kyautar sabuwar Toyota Camry.

DUBA WANNAN: Bidiyo: An kama wani dumu-dumu yana ƙoƙarin yin zina da matar mai gidansa

Ya ce: "Muna son matasa suyi koyi da irin wannan halin. Samun irin wannan gaskiyar da kishin ƙasa yana da wahala daga matashin da ba shi da aikin yi da zai iya siyar da wayan ...

"Ya kamata a riƙa karrama irin su a kuma rika saka musu da alheri saboda gaskiyarsu."

Obi ya yi wa ƙasar na APC godiya bisa kyautar da ya yi masa.

Ya ce: "Kyautar sabuwar motar da aka yi masa zai taimaka masa ya fara aikin da ya ke ƙauna kuma zai ƙarfafa wa wasu gwiwa su zama masu gaskiya."

Ifeanyichikwu ya yi wa Onyeka godiya bisa karamcin da ya yi masa. Ya yi alƙawarin zai ƙarfafa wa wasu gwiwa su rike gaskiya da amana a rayuwarsu.

Matashin ya yi wa Obi godiya saboda watsa labarinsa da kuma ɗaukan sa tamkar ɗan uwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel