Yanzu-yanzu: An sace kofin gasar kwallon Afrika AFCON a hedkwatar CAF

Yanzu-yanzu: An sace kofin gasar kwallon Afrika AFCON a hedkwatar CAF

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa an sace kofin zinarin gasar kwallon nahiyar Afrika a hedkwatar CAF dake kasar Masar, Goal.com ta ruwaito.

An baiwa kasar Masar daman cigaba da rike kofin din-din-din saboda sun samu nasarar lashe gasar sau uku a jere.

Amma, tsohon shugaban hukumar kwallon Masar, Magdi Abdelghani, ya yi bayanin cewa kofin ya kone a gobarar da ta cinye hedkwatar a 2013.

Tsohon mataimakin shugaban hukumar kwallon kasar, Ahmed Shobeir, ne ya bayyana cewa an nemi kofin an rasa yayinda ake cikin gina wani gidan tarihin dukkan kofunan da kasar ta mallaka.

Amma tsohon ma'aikacin FIFA, Abdelgahni ya tabbatar da cewa kofin na daya daga cikin abubuwan da suka kone shekaru bakwai da suka gabata.

"Jami'an kwamitin da ke zama bayan shekaru biyar kuma suka jagorantar hukumar yanzu sun yi mamakin rashin ganin kofin" Shobeir ya bayyana a hirar tasgar 'On Time Sports'.

"Yanzu an kaddamar da bincike."

Da farko an ce kofin na hannun tsohon dan kwallon Ahmad Hassan wanda ya jagoranci yan kwallon wajen nasarar lashe gasar a 2006, 2008 da 2010, amma ya musanta hakan.

Ana buga wasan kwallon kasashen nahiyar Afrika ne bayan kowani shekara biyu. Kasar Algeriya ce ta lashe na gasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel