Daukan sabbin yan sanda: An tantance matasa sama da 13,000 a jihar Kano

Daukan sabbin yan sanda: An tantance matasa sama da 13,000 a jihar Kano

Hukumar yan sanda a jihar Kano ta ce kawo yanzu an tantance matasa 13,048 dake neman gurbin shiga aikin dan sanda tsawon kwanaki 11 yanzu a jihar.

Kakakin hukumar, DSP Abdullahi Haruna, ya bayyana hakan a jawabin da yayi yayinda yake tsokaci kan shirin tantance masu neman gurbin shiga aikin a Kano ranar Juma'a.

Haruna ya ce an tantance matasan kananan hukumomi 40 cikin 44 na jihar, The Punch ta ruwaito.

"Daga 24 ga Agusta zuwa yanzu, an samu nasarar tantance mutane 13,048 daga kananan hukumomi 40 cikin 44 na jihar." Yace

Haruna ya ce an tantance matasa 1,475 daga kananan hukumomin Takai, Tarauni, Tofa da Tsanyawa ranar Alhamis, kuma za'a kammala ranar Juma'a.

Kakakin ya lissafo kananan hukumomin da za'a karasa tantancewar ga wadanda basu samu daman halarta ba.

Sun hada Tudun Wada, Warawa, Wudil da Ungogo.

A cewarsa, hukumar na takatsantsan kuma tana bin ka'idojin da aka gindaya don kare kai daga cutar Korona.

Daukan sabbin yan sanda: An tantance matasa sama da 13,000 a jihar Kano
Daukan sabbin yan sanda: An tantance matasa sama da 13,000 a jihar Kano
Source: UGC

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya nada dan Arewa, Mairiga, babban mukami

Daukan sabbin yan sanda: An tantance matasa sama da 13,000 a jihar Kano
Daukan sabbin yan sanda: An tantance matasa sama da 13,000 a jihar Kano
Source: UGC

DUBA WANNAN: Buhari ya mikawa gwamnan Ondo tutar takara karo na biyu karkashin jam'iyyar APC

Daukan sabbin yan sanda: An tantance matasa sama da 13,000 a jihar Kano
Daukan sabbin yan sanda: An tantance matasa sama da 13,000 a jihar Kano
Source: UGC

A wani labarin daban, Jaridar Daily Trust ta fitar da cikakken labari na wani jami’in ‘yan sanda da ya kashe mutane biyu a dalilin zarginsu da ake yi da laifin satar kaji a Bauchi.

Kwanakin baya dakarun ‘yan sanda su ka kama Ibrahim Kapala, Ibrahim Babangida da Abdulwahab Bello, a karshe 'yan sanda su ka yi sanadiyyar mutuwarsu.

Rahoton da aka fitar ya ce ana zargin DPO Baba Ali Mohammed ne ya yi ta dukan wadannan Bayin Allah, a sanadiyyar haka ne su ka ce masa ga garin ku nan.

Abdulwahab Bello wanda yanzu an karya masa duka kafafunsa shi ne ya taki sa’a, amma kwanakin abokansa sun kare a hannun wannan mugun jami’i, Baba Ali.

Jami’an tsaro sun yi ram da wadannan mutane uku ne da sunan sun saci kajin wani tsohon ‘dan sanda da ya yi ritaya. Laifin Bello shi ne ya hada su da mai sayen kajin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel