Da duminsa: Messi zai cigaba da zama a kungiyar Barcelona

Da duminsa: Messi zai cigaba da zama a kungiyar Barcelona

Zakaran ɗan kwallo Lionel Messi yana iya sanar da cigaba da zamansa a kungiyar Barcelona kowanne lokaci daga yanzu.

Ɗan kwallon da ya lashe Ballon D'or har sau shida ya sanar da kungiyarsa cewa yana son barin ƙungiyar a makon da ta gabata.

Amma kungiyar ta kasar Spain da dage cewa ba za ta saki kyaftin ɗin ta ba har sai idan za a siye shi a kan kudi a kalla €700m wanda ya yi kwatankwacin fam miliyan 624 .

Da duminsa: Messi zai cigaba da zama a Barcelona
Da duminsa: Messi zai cigaba da zama a Barcelona
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Bidiyo: An kama wani dumu-dumu yana ƙoƙarin yin zina da matar mai gidansa

Kungiyar Manchester City kuma da ya ke son tafiya ba za ta iya biyan wannan kuɗin ba.

Wani fitaccen ɗan jarida a Spain, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, "Lionel Messi yana daf da sanarwa a hukumance: zai cigaba da zama a Barcelona bayan ƙungiyar ta ƙi siyar da shi ƙasa da €700m."

Majiyoyi da dama sun tabbatar da wannan batun inda suka ce nan ba da dade wa ba Lionel Messi zai sanar da kansa.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, shugaban SCOAN, Fasto T.B Joshua, ya shawarci kaftin din kungiyar Barcelona, Lionel Messi, a kan tababar da ta kunno kai a tsakaninsa da mahukuntan kulob din Barca.

Messi, haziki kuma fitaccen dan wasan kwallon kafa mai shekaru 33, ya shafe kusan shekaru 20 ya na bugawa kungiyar Barcelona wasa.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa a kan wannan balahira a shafinsa na Twitter, TB Joshua ya bukaci Messi a kan kar ya bar kungiyar Barcelona cikin fushi da bacin rai.

Sakon TB Joshua na cewa;

"Ba shawara ce mai kyau ba a ce Lionel Messi ya bar Barcelona cikin fushi da bacin rai. Ba zai yiwu a kulla zumunci ko wata alaka ta kirki da mutumin da aka yi rabuwar baran-baran da shi ba. Wanna ita ce shawarar da zan bawa Messi. Tarihi zai mana hukunci," kamar yadda ya wallafa.

Sai kuma gashi dai a yanzu Messi ya sanar da cewa zai cigaba da zama a kungiyar ta Barcelona saboda ya gaza cika wasu ka'idoji da ke cikin kwantiraginsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel