Da duminsa: Shugaba Buhari ya nada dan Arewa, Mairiga, babban mukami

Da duminsa: Shugaba Buhari ya nada dan Arewa, Mairiga, babban mukami

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ibrahim Mairiga, matsayin babban sakataren hukumar basussukan gidajen tarayya (FGSHLB).

Shugabar ma'aikatan Najeriya, Folasade Yemi-Esan, ta bayyana hakan ne a wani jawabin da Diraktar labaranta, Misis Olawunmi Ogunmusunle, ta sake ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja.

A cewar Yemi-Esan, wa'adin Ibrahim Mairiga na shekara hudu a kujerar ya fara ne tun daga ranar 24 ga Yuli, Leadership ta ruwaito.

Ta ce wannan sabon mukami da aka bashi na bukatar jajircewa, mayar da hankali, da kokari domin cimma manufar hukumar.

Yemi-Esan ta shawarci Mairiga yayi amfani da kwarewar da ya samu da ilimi wajen yin aikin da ke gabansa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa Mairiga dan asalin jihar Gombe ne, kuma yayi karatun Majistir dinsa a Jami'ar Maiduguri kuma yayi Digiri a jami'ar Bayero dake Kano.

Gabanin yanzu, ya kasance Diraktan aikin yi.

KU KARANTA: Buhari ya mikawa gwamnan Ondo tutar takara karo na biyu karkashin jam'iyyar APC

Da duminsa: Shugaba Buhari ya nada dan Arewa, Mairiga, babban mukami
Da duminsa: Shugaba Buhari ya nada dan Arewa, Mairiga, babban mukami
Source: Twitter

A bangare guda, A ranar Alhamis ne Karamin Ministan Kasafi da Tsarin Kasa, Clement Agba, ya bayyana cewar a watan Disamba ne za a gabatar da sabon salon tsarin bunkasa tattalin arzikin kasa wanda zai yi tasiri har tsawon shekaru hudu.

Ministan ya ce Shugaba Buhari ne zai gabatar da wannan tsarin wanda yunkuri ne na farfado da tattalin arziki wanda ya riga ya durkushe a wannan shekarar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ministan ya kara da cewar, tsarin an kasa shi gida biyu, gajeran zango wanda zai yi tasiri tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025 da kuma shekarun 2026 zuwa 2030.

Sai kuma tsari na dogon zango wanda hasashe ne na shekarar 2050.

DUBA WANNAN: Babu dan Adam ko daya dake rayuwa a kananan hukumomin Borno uku - Kakakin majalisar Borno

Ministan ya yi wannan jawabi ne a taron karawa juna sani da hukumar ta sa ta shirya. Ya kuma ce wannan tsarin zai sanya Najeriya cikin jerin kasashe guda 20 mafiya arziki a duniya.

"Wannan tsarin shi ne zai yi jagoranci wurin kasafin kasa na shekarar 2021", In ji Ministan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel