Babu dan Adam ko daya dake rayuwa a kananan hukumomin Borno uku - Kakakin majalisar Borno

Babu dan Adam ko daya dake rayuwa a kananan hukumomin Borno uku - Kakakin majalisar Borno

Babu dan Adam ko guda dake zaune a kananan hukumomin jihar Borno uku saboda matsalan rashin tsaro, kakakin majalisar dokokin jihar, AbdulKareem Lawan, ya bayyana ranar Alhamis.

Kananan hukumomin sune Guzamala, Marte da Abadam, dukkansu na arewacin jihar kuma sun fuskanci kalubale iri-iri sakamakon yakin Boko Haram da yaki ci yaki cinyewa tsawon shekaru 11 yanzu.

Kakakin ya ce a karamar hukumar Guzamala, mai hedkwata A Gudumbali, kuma mai nisan kilomita 125 da Maiduguri, babu Soja ko mai farin hula daya dake rayuwa a garin, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce akwai bukatar gwamnatin taraya ta kara yawan Sojojin domin kare Arewacin Borno saboda masu zama a sansanin gudun Hijra su koma muhallansu.

Babu dan Adam ko daya dake rayuwa a kananan hukumomin Borno uku - Kakakin majalisar Borno
Babu dan Adam ko daya dake rayuwa a kananan hukumomin Borno uku - Kakakin majalisar Borno
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Buhari ya mikawa gwamnan Ondo tutar takara karo na biyu karkashin jam'iyyar APC

Lawan ya yi wannan jawabi ne yayinda yake karban bakuncin tawagar kungiyar matasan Guzamala karkashin jagorancin shugabansu, Babagana Alkali, a Maiduguri.

Ya ce ya zama wajibi yayi magana saboda duniya ta san halin da ake ciki a Guzamala, Marte da Abadam.

"Abin ya tayar min da hankali da safen nan da na saurari jawabin shugaban tawagar." Yace

"A matsayina na wakilinku, wajibi ne in bayyana muku abinda ake ciki."

"Karamar hukumar Guzamala ba tada nisa da birnin jihar; muna da dakatai biyu da masu gari 16 kuma dukkansu sun dawo nan Maiduguri."

"Muna da garuruwan 170 a Guzamala amma a yanzu haka da nike muku magana, babu rai daya; Soja ko mai farin hula ko wani jami'in tsaro dake rayuwa a Guzamala gaba daya."

"Babu mai farin hula ko daya a Abadam; akwai Sojoji a hedkwatan karamar hukumar (Malam Fatori) dake kare garin."

"Yawancin mutanen Adabam sun gudu kasar Nijar ko garin Monguno."

"Hakazalika idan kaje Marte. Babu mai farin hula ko daya a garin gaba daya."

"Saboda haka ina kira ga gwamnati ta tura karin Sojoji arewacin jihar Borno."

"Ina kira ga gwamnatin tarayya ta hanzarta dubi cikin lamarin rashin tsaron da jihar ke fama da shi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel