Da ɗumi-ɗumi: Ƴan bindigan sun sace Sarkin Fulanin Ilorin

Da ɗumi-ɗumi: Ƴan bindigan sun sace Sarkin Fulanin Ilorin

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari asibitin koyarwa ta jami'ar Ilorin a ranar Alhamis 3 ga watan Satumba sun sace Sarkin Fulanin Ilorin, Usman Adamu Harɗo.

Ƴan bindigan sun kai harin ne misalin karfe 8 na safe kamar yadda Linda Ikeji ta ruwaito.

Rahotanni sun ce Sarkin Fulanin yana hanyarsa ta zuwa banki ne a cikin mota tare da ɗansa Babangida yayin da wasu ƴan bindigan suka tare motarsu.

Da ɗumi-ɗumi: Ƴan bindigan sun sace Sarkin Fulanin Ilorin
Da ɗumi-ɗumi: Ƴan bindigan sun sace Sarkin Fulanin Ilorin
Source: UGC

DUBA WANNAN: Bidiyo: An kama wani dumu-dumu yana ƙoƙarin yin zina da matar mai gidansa

Wani ganau ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa;

"Sun buƙaci ya fito daga motarsa ya shiga motarsu, an gano cewa yana ɗauke da wasu kudade da zai kai banki a lokacin da suka sace shi.

"Daga bisani an gano motarsa da wayarsa a cikin motar, motar da wayan suna wurin yan sanda a yanzu."

Matar Usman, Hajiya Aina'u Usman ta tabbatar da sace shi, ta ce masu garkuwa da mutanen sunyi magana da harshen hausa kuma kaftani suka saka.

Ta ce;

"Ba su tafi da ɗansa Babangida ba. Ya dawo gida.

"Ya shaida mana cewa wasu mutane uku ɗauke da bindiga ne suka fito daga motarsu suka tilasta wa miji na ya bi su.

"Ya roke su su karɓi kuɗin su ƙyale shi ya tafi amma suka ƙi yarda, sun ce dama sun daɗe suna neman shi.

"Da harshen Hausa suka yi magana amma sun rufe fuskokinsu kuma kaftan suka saka."

Ta kuma bayyana cewa mijinta yana fama da wata cuta da bata faɗi irinta kuma ta roki a ceto shi.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji cewa an gano jami'an hukumar kula da dokokin tuki na jihar Legas, LASTMA, su biyu suna faɗa da fasinjoji a wani mota da suka fito daga Ikeja zuwa Obalende.

Jami'an na LASTMA da kayan aikinsu ke dauke da sunayen E.A. Fagbuyi da N. Oladega sun tare direban motan a toll gate na 7 up da ke kusa da Berger road a Legas.

Sun yi zargin cewa tun a makon da ya gabata ya ke canja hanya don kada ya hadu da su kuma suka bukaci ya biya su kuɗi saboda hakan.

Yaron motar (kwandasta) ya shaida wa wakilin Premium Times a cikin motar cewa suna neman direban ya basu toshiyar baki ta Naira 100 ne.

Sai dai lamarin ya ɗauki sabon salo bayan Fagbuyi ya karbe motar kuma ya nufa wata hanya daban ba inda fasinjojin za su tafi ba.

Daga nan ne kuma fasinjojin da ke cikin motar suka harzuƙa suka nuna ƙin amincewarsu da hakan ya janyo musayar kalamai har aka kaure da dambe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel