Bidiyo: Ƴan bindiga sun hallaka yayin da sojoji suka kai musu hari ta sama a dajin Kuduru da Kuyambana a Kaduna

Bidiyo: Ƴan bindiga sun hallaka yayin da sojoji suka kai musu hari ta sama a dajin Kuduru da Kuyambana a Kaduna

- Dakarun sojojin saman Najeriya sun sake yin nasarar kai hari a wasu maɓuyar ƴan bindiga a jihar Kaduna

- Sojojin na Operation Thunder Strike sun kai hari a sansanin ƴan bindiga a dajin Kuduru da Kuyambana

- Sojojin ta hanyar amfani da jiragen yaƙi sunyi nasarar halaka ƴan bindiga da dama tare da lalata gine-ginensu

Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce dakarun ta na Operation Thunder Strike sun kashe ƴan bindiga masu yawa a harin da ta kai sansaninsu da ke dajin Kuduru da Kuyambana a jihar Kaduna.

Kakakin rundunar ta musamman, Manjo Janar John Enenche ne ya sanar da hakan ta shafin rundunar na Twitter a ranar Juma'a a Abuja.

Bidiyo: Ƴan bindiga sun hallaka yayin da sojojin suka kai musu hari ta sama a dajin Kuduru da Kuyambana a Kaduna
Bidiyo: Ƴan bindiga sun hallaka yayin da sojojin suka kai musu hari ta sama a dajin Kuduru da Kuyambana a Kaduna. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

Ya ce dakarun sojojin sun samu wannan nasarorin ne sakamakon hare-haren da suka kai a ranakun Laraba da Alhamis.

Enenche ya ce sojojin sun samu sahihan bayanan sirri da ke nuna yan ta'addan na amfani da wuraren don shirya kai hari kafin aka far musu.

Ya ce an kai harin a maɓuyar ƴan ta'addan a dajin Kuduru ne na'urar leƙen asiri ya nuna akwai ƴan bindiga da dama a cikin gine-ginen da ke dajin.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarayya ta amince da buɗe makarantu a Najeriya

A cewarsa, rundunar dakarun saman ta NAF ta aike da jiragen yaƙi da jirgi mai saukan ungulu masu ɗauke da bindiga zuwa wurin.

"Jiragen yaƙin sun yi ta ruwan bama-bamai ɗaya bayan ɗaya a inda gine-ginen suke inda suka kashe da dama tare da lalata sansanin.

"A dajin Kuyambana inda aka hango wasu ƴan bindiga tare da shanu da suka sace kusa da wasu bukoki, jiragen NAF da jirage masu saukan ungulu sun musu ruwan wuta inda suka yi nasarar lashe da dama cikin su," in ji shi.

A wani labarin daban, kun ji kwamishinan 'yan sandan jihar Neja, Adamu Hassan, ya yi karin bayani dangane da harin da 'yan bindiga suka kai wani banki da ke garin Kagara na jihar Neja a ranar Laraba.

Da ya kai ziyarar gani da ido zuwa Kagara ranar Alhamis, Hassan ya sanar da cewa rundunar 'yan sanda ta kashe shidda daga cikin 'yan bindigar da suka kai hari garin ranar Laraba.

Kazalika, kwamishinan ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe dan sanda guda daya, wani jami'in tsaro na kamfani, dan bijilanti da kuma wani mutum.

Ya kara da cewar wani yaro guda daya ya mutu sakamakon razanar da ya yi a lokacin da 'yan bindigar suka kai harin.

Kwamishina Hassan ya ce 'yan bindigar sun tsere sun bar baburansu guda hudu bayan sun ga jami'an 'yan sanda na kokarin cimmasu a yayin da suke musayar wuta.

"Na jinjinawa ma'aikatanmu da ke aiki a ofishin 'yan sanda na Kagara saboda karfin gwuiwar da suka nuna wajen tunkarar 'yan bindigar ba tare da tsoron cewa suna dauke da muggan makamai ba.

"Hedikwatar 'yan sanda ta jiha zata cigaba da bayar da dukkan gudunmawar da ta dace ga jami'anta a kowanne bangare na jihar Neja domin yaki da 'yan ta'adda da batagari," a cewar Kwamishinan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel