Karin kuɗin man fetur: APC ta ce gwamnati ƴan ƙasa ta ke yi wa aiki

Karin kuɗin man fetur: APC ta ce gwamnati ƴan ƙasa ta ke yi wa aiki

Jam'iyyar APC mai mulki ta yi kira ga babban jam'iyyar adawa ta PDP ta farga ta gane cewa Najeriya ta canja kuma ƴan ƙasa ake yi wa aiki ba wasu tsirarun ba.

Mista Yekini Nabena, mataimakin sakataren watsa labarai na ƙasa na jam'iyyar ne ya yi wannan kirar a ranar Laraba a Abuja.

Ya yi wannan sanarwar ne a matsayin martani game da sukar ƙarin kuɗin lantarki da na man fetur da gwamnatin tarayya ta yi daga N143 zuwa N151.

A baya, PDP cikin wata sanarwa da sakataren watsa labaran ta na ƙasa, Kola Ologbondiyan ya fitar ta nuna ƙin amincewarta da ƙarin farashin.

Karin kuɗin man fetur: APC ta ce gwamnati ƴan ƙasa ta ke yi wa aiki
Karin kuɗin man fetur: APC ta ce gwamnati ƴan ƙasa ta ke yi wa aiki
Asali: Twitter

"PDP ba ta amince da sabon ƙarin kuɗin man fetur zuwa N151 duk lita ba ta lantarki zuwa N66 duk kilowatt a ƙarƙashin gwamnatin APC," in ji Ologbondiyan.

Ya bukaci a mayar da farashin yadda suke a baya domin kare kasar daga afkawa cikin fitina.

A cewarsa, ƙarin farashin zai janyo ƙarin kuɗin ayyuka da kayan masarufi tare da tsananta rayuwa ga ƴan kasar.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarayya ta amince da buɗe makarantu a Najeriya

Amma APC ta ce an yi ƙarin kuɗin man fetur ɗin da lantarki ne da nufin ƙasar da alheri.

"APC ta ji wata sanarwa mara kan gado da PDP ta fitar a kan ƙarin kuɗin man fetur da lantarki a kasar."

Nabena ya tunatar da cewa gwamnatocin PDP da suka gabata ne suka lalata kasar da rashawa da sunan tallafin man fetur.

Ya yi kira da PDP ta bawa kanta mamaki da ƴan Najeriya ta lalaɓi abokanta da suka tsere da kudin tallafin man fetur su dawo da shi, har da wadanda suke ɓuya a ƙasashen waje.

Ya ce a karkashin gwamnatin Shugaba Buhari, ba a samun mummanan layin mai sakamakon ƙarancin man fetur da aka saba yin wahalarsa a baya.

A cewar Nabena, sabon farashin da man fetur ƙarkashin gwamnatin APC ya haifar da tsafta a bangaren na man fetur tare da inganta ayyuka.

Ya kuma kara da cewa hakan ya sa an samu wadatar man fetur a dukkan faɗin ƙasar.

Ya ce akwai yiwuwar PDP ba ta san cewa gwamnatin tarayya ta janye haraji a kan shigo da mita na wutar lantarki na tsawon shekara ɗaya ba.

A cewarsa, an yi hakan ne domin bawa kamfanonin samar da lantarkin damar shigo da mitocin cikin sauƙi a kuma sayar wa ƴan Najeriya da sauƙin.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar shima ya yi tsokaci a kan karin kudin man fetur din inda ya ce gwamnati ba ta yi tunani ba kafin ta yi karin.

Ya ce karin bai dace ba duba da cewa mutanen kasar suna cikin mawuyacin hali sakamakon kulle ta annobar korona da ta shafi sana'o'insu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel