An yankewa wani mutumi hukuncin kisa bayan an tsinci gawarwakin wasu mata guda biyu a cikin firjin shi

An yankewa wani mutumi hukuncin kisa bayan an tsinci gawarwakin wasu mata guda biyu a cikin firjin shi

Wani mutumi da ya kashe wasu mata guda biyu ya boye gawarwakin su a cikin firji yana fuskantar hukuncin kisa

Mutumin mai suna Zahid Younis an yanke masa hukuncin kisa, ta hanyar yin shekaru 38 a gidan yari.

Gawarwakin Henriett Szucs da kuma na Mihrican Mustafa an samo su a gidan Zahid a garin Canning, yankin gabashin London, a watan Afrilun shekarar 2019.

An ruwaito cewa yayi rikici da matan kafin ranar da ya kashe su duka su biyu.

Gawar daya daga cikinsu Henriett Szucs na ajiye a cikin firji tsawon shekara uku kafin 'yan sanda suka gano ta gidan saurayin dan shekara 36 a gabashin London.

An yankewa wani mutumi hukuncin kisa bayan an tsinci gawarwakin wasu mata guda biyu a cikin firjin shi
An yankewa wani mutumi hukuncin kisa bayan an tsinci gawarwakin wasu mata guda biyu a cikin firjin shi
Asali: Facebook

Ms Szucs, mai shekaru 34 da take 'yar asalin kasar Hungary, ganin da aka yi mata na karshe shine a watan Agustan shekarar 2016, kuma an tabbatar cewa ta tafi ta zauna da Younis ne a gidansa.

Mace ta biyun kuma wacce take tana da 'ya'ya guda uku mai suna Mihrican Mustafa, mai shekaru 38, ita ma ba a kara jin duriyarta ba tun a cikin watan Mayun shekarar 2018.

Ms Szucs da Ms Mustafa, duka mata ne da suke yin wata irin rayuwa, inda suke barin gidajensu, shan miyagun kwayoyi da sauransu, kamar dai yadda kotun ta samu rahoto.

An ruwaito cewa Younis ya sayi wannan firji ne jim kadan bayan ya kashe Ms Szucs saboda kawai ya ajiye gawarta a ciki.

KU KARANTA: Tashin hankali: Wani mutumi ya fillewa mahaifiyarshi kai da takobi ya boye kan a cikin firji

Sufeton 'yan sanda da ya samu damar shiga gidan ya bayyana cewa sai da suka bude firjin ta karfin tsiya sannan suka gano abinda ke ciki.

Yanayin wannan lamari ya sanya baza a iya gano ainahin yadda aka kashe su ba, amma kuma shaida ta nuna cewa sai da aka ci zarafinsu kafin a kashe su.

Duka sun samu karaya a hakarkarinsu, inda ita kuma Ms Szucs ta samu mummunan rauni a kanta.

Kotun ta gano cewa dama can Younis yana da wannan halayya ta kaiwa abokanan shi hari.

Younis wanda aka fi sani da Boxer, yaki amincewa da shi ya kashe su, amma ya yarda cewa ya ajiye su a cikin firji.

Ya ce lokacin da Ms Szucs ta mutu a gidan shi ya fita, kuma tsoro ya hana shi sanar da 'yan sanda halin da ake ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel