Jami'o'in Najeriya 6 na cikin manyan jami'o'i 1000 mafi inganci a duniya (Jerinsu)

Jami'o'in Najeriya 6 na cikin manyan jami'o'i 1000 mafi inganci a duniya (Jerinsu)

Jami'ar Ibadan dake jihar Oyo (UI) ta kwace matsayin jami'ar Covenant na jami'a mafi inganci a Najeriya a sabon jadawalin jami'o'i mafi kyau a duniya da jaridar Times ta saki.

A 2019, jami'an Covenant ce ta lashe matsayin jami'a mafi ingancin ilmi da kotarwa a Najeriya.

Amma a sakamakon da aka saki na bana, jami'ar Ibadan ta samu maki 401-500.

Ga jerin jami'o'in Najeriya 6 da suka samu shiga jerin manyan jami'o'in duniya:

Jami'ar Ibadan UI (401 – 500)

Jami'ar jihar Legas LASU (501 – 600)

Jami'ar Legas UNILAG (601- 800)

Jami'ar Covenant (801 – 1000)

Jami'ar Najeriya UNN (1001+)

Jami'ar Obafemi Awolowo OAU (1001+)

Jami'o'in Najeriya 6 na cikin manyan jami'o'i 1000 mafi inganci a duniya (Jerinsu)
Jami'o'in Najeriya 6 na cikin manyan jami'o'i 1000 mafi inganci a duniya (Jerinsu)
Source: UGC

A karo na biyar, jami'ar Oxford a kasar Ingila ce zakarar jami'o'in duniya yayinda jami'ar Cambridge ta sauke daga na uku zuwa na shida bana.

Ga jerin jami'o'in duniya na gaba 10:

(1) Jami'ar Oxford (UK)

(2) Jamiar Stanford (US)

(3) Jamiar Harvard (US)

(4) California Institute of Technology (US)

(6) Massachusetts Institute of Technology MIT (US)

(7) Jami'ar Cambridge (UK)

(8) Jami'ar California, Berkeley (US)

(9) Jami'ar Yale (US)

(10) Jami'ar Princeton (US)

(9) University of Chicago (US)

A bangare guda, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce gwamnatocin jihohi da shugabannin makarantu su fara shirin buɗe makarantun baki daya, jaridar The Punch ta ruwaito.

Tun a watan Maris ne aka rufe makarantun kasar a matsayin matakin dakile yaduwar annobar coronavirus.

Amma gwamnatin tarayyar ta sanar da cewa, daliban ajin ƙarshe na firamare da sakandare su koma makaranta a ranar 4 watan Agusta domin rubuta jarrabawar fita.

A yayin jawabinsa a ranar Alhamis, Shugaban Kwamitin Yaki da Covid-19 na shugaban ƙasa, Dr Sani Aliyu, ya ce kwamitin ta bayar da shawarar bude makarantu.

Aliyu ya yi wannan jawabin ne a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Aliyu ya ce makarantu da suka hada da na kula da yara, firamare, sakandare da na gaba da sakandare su fara shirin buɗe wa a wannan matakin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel