Jami'an yan sanda sun damke yan bindiga 50 a Katsina, sun kwace shanu 220

Jami'an yan sanda sun damke yan bindiga 50 a Katsina, sun kwace shanu 220

Hukumar yan sandan jihar Katsina a ranar Alhamis ta bayyana yan bindiga kimanin 50 da ta kama tare da shanu 220 da suka sace na jama'a.

Kwamishanan yan sandan jihar, Sanusi Buba Sanusi, ya bayyana hakan ga manema labarai, Sahara Reporters ta ruwaito.

Ya ce an kama yan bindigan a farautar barayin shanu, yan fashi da masu garkuwa da mutane da hukumar keyi.

Sauran kayayyakin da aka samu nasaran daga hannunsu a cewar Kwamishanan su hada da bindiga AK47 guda 9, kananan bindigogi 20, motoci 2 da babura 20.

Yace: "A cikin wannan lokaci, hukumar ta gudanar hare-haren leken asirin a wurare daban-daban a kananan hukumomin da hare-hare a addaba, kuma mun damke yan bindigan da suka addabi jihar da dama."

"Hakazalika, mun samu kudi N685,000 a hannunsu, an kashe 15 tare da ceton mutane 20 da suka sace."

Jami'an yan sanda sun damke yan bindiga 50 a Katsina, sun kwace shanu 220
Jami'an yan sanda sun damke yan bindiga 50 a Katsina, sun kwace shanu 220
Source: Facebook

KU KARANTA: Jami'o'in Najeriya 6 na cikin manyan jami'o'i 1000 mafi inganci a duniya (Jerinsu)

A wani labarin, Kwamishinan 'yan sandan jihar Neja, Adamu Hassan, ya yi karin bayani dangane da harin da 'yan bindiga suka kai wani banki da ke garin Kagara na jihar Neja a ranar Laraba.

Da ya kai ziyarar gani da ido zuwa Kagara ranar Alhamis, Hassan ya sanar da cewa rundunar 'yan sanda ta kashe shidda daga cikin 'yan bindigar da suka kai hari garin ranar Laraba.

Kazalika, kwamishinan ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe dan sanda guda daya, wani jami'in tsaro na kamfani, dan bijilanti da kuma wani mutum.

Ya kara da cewar wani yaro guda daya ya mutu sakamakon razanar da ya yi a lokacin da 'yan bindigar suka kai harin.

Kwamishina Hassan ya ce 'yan bindigar sun tsere sun bar baburansu guda hudu bayan sun ga jami'an 'yan sanda na kokarin cimmasu a yayin da suke musayar wuta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel