Yanzu-yanzu: FG ta amince a buɗe sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima

Yanzu-yanzu: FG ta amince a buɗe sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bawa Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidima, NYSC, ta fara shirye-shiryen buɗe sansanin horaswarta a dukkan faɗin ƙasar.

Shugaban kwamitin ƴaki da korona ta shugaban ƙasa, Dakta Sani Aliyu ne ya bayar da wannan sanarwar a ranar Alhamis yayin jawabin kwamitin a Abuja.

Aliyu ya ce hukumar ta NYSC ta fara shirin buɗe sansanonin ta tare da inganta matakan kare yaɗuwar cutar da zarar makarantu sun buɗe.

Ya ce, "A bangaren hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima, NYSC ta ɗora a kan matakan kariya da ake da su a yanzu ta fara shirin buɗe sansanonin ta da zarar an buɗe makarantu.

"Muna kan tsara dokokin ta yadda ba za a samu ɓullar annobar korona ba da zarar an buɗe sansanonin."

Ku saurari cikakken rahoton ...

Yanzu-yanzu: FG ta amince a buɗe sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima
Yanzu-yanzu: FG ta amince a buɗe sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima. Hoto daga The Punch
Source: UGC

KU KARANTA: Soja ya buɗe wa ƙananan yara wuta a kusa da fadar shehun Borno, ya kashe ɗaya

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel