Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarayya ta amince da buɗe makarantu a Najeriya
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce gwamnatocin jihohi da shugabannin makarantu su fara shirin buɗe makarantun baki daya, jaridar The Punch ta ruwaito.
Tun a watan Maris ne aka rufe makarantun kasar a matsayin matakin dakile yaduwar annobar coronavirus.
Amma gwamnatin tarayyar ta sanar da cewa, daliban ajin ƙarshe na firamare da sakandare su koma makaranta a ranar 4 watan Agusta domin rubuta jarrabawar fita.
A yayin jawabinsa a ranar Alhamis, Shugaban Kwamitin Yaki da Covid-19 na shugaban ƙasa, Dr Sani Aliyu, ya ce kwamitin ta bayar da shawarar bude makarantu.
Aliyu ya yi wannan jawabin ne a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Aliyu ya ce makarantu da suka hada da na kula da yara, firamare, sakandare da na gaba da sakandare su fara shirin buɗe wa a wannan matakin.
"Amma muna shawartar jihohi da suyi nazarin hatsarin da ke tattare da buɗe makarantun, su tabbatar da bin dokoki a dukkan matakai.
"Amma dai a halin yanzu, makarantu ba za su buɗe ba har sai an kammala gudanar da nazarin idan kuma za a bude zai fi dace wa a bude daga mataki zuwa mataki domin kiyaye yiwuwar ɗalibai su koma gida su yaɗa wa masu cutar."

Asali: Twitter
Ku saurari ƙarin bayani ...
KU KARANTA: Soja ya buɗe wa ƙananan yara wuta a kusa da fadar shehun Borno, ya kashe ɗaya
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng