Tura ta kai bango: 'Yan Najeriya sun harzuka, sun mayarwa Buhari martani

Tura ta kai bango: 'Yan Najeriya sun harzuka, sun mayarwa Buhari martani

Dubban 'yan Najeriya sun yi tururuwa wajen bayyana ra'ayinsu tare da mayarwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, martani a kan kara farashin man fetur da kuma tsadar kayan abinci.

Hauhawar farashin kayan abinci da kara farashin litar man fetur da karin kudin wutar lantarki sun harzuka 'yan Najeriya, lamarin da yasa jama'a da dama ke bayyana nadamarsu tare da yin da na sanin goyon bayan gwamnatin Buhari.

A ranar Laraba ne kafafen yada labarai su ka wallafa labarin cewa kamfanin tallar man fetur mallakar gwamnatin tarayya (PPMC) ya sanar da kara farashin litar mana fetur zuwa N151 kowacce lita.

Kafin fitowar sanarwar kara farashin man fetur, hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasa (NERC) ta sanar da yin karin kudin wutar lantarki daga N27.2 zuwa N66 a kan kowanne KW a ranar Talata, 1 ga watan Satumba.

Da ya ke martani a kan karin kudin wutar lantarki, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, ya ce ko kadan bai kamata karin kudin ya zo a irin wannan lokaci da jama'a suke a galabaice ba.

Tura ta kai bango: 'Yan Najeriya sun harzuka, sun mayarwa Buhari martani
Buhari da Osinbajo yayin yakin neman zabe
Asali: UGC

A cewa Atiku, 'yan Najeriya tallafi suke bukata domin farfadowa daga halin matsin da suka shiga sakamakon dokar kulle da aka saka saboda barkewar annobar korona.

DUBA WANNAN: Yadda zamu narka biliyan N600 a bangaren noma - Minista Sabo Nanono

"Ban yarda da karin kudin wutar lantarki ba. 'Yan Najeriya tallafi suke bukata domin samun damar farfadowa. Kudi ba ya shiga hannun jama' na tsawon lokaci sakamakon dokar kulle, wanda hakan kuma ba laifinsu bane. Bai kamata a yi karin kudi a irin wanann lokacin ba," a cewarsa.

A nasa bangaren, tsohon sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Kwamred shehu Sani, ya yi wa gwamnati shagube a kan abubuwan da farashinsu ke karuwa da kuma abubuwan da darajarsu ke karyewa a gwamnatin Buhari.

"Abubuwan da ke yin sama; rancen kudi daga kasashen waje, kudin wutar lantarki, farashin man fetur, farashin shinkafa, tsadar rayuwa.

"Abubuwan da ke yin kasa; darajar Naira, asusun ajiyar gwamnati na kasar waje," kamar yadda Shehu Sani ya wallafa.

Tuni wani sashe na matasan Najeria su ka nemi Atiku ya jagoranci zanga-zanga domin nunawa gwamnati cewa tura ta kai bango, rayuwa kullum kara wahala ta ke yi, amma duk da haka gwamnati na kara gallazawa jama'a.

Tambayar da wasu da dama ke cigaba da yi wa shugaba Buhari da jam'iyyar APC shine ina canjin da suka yi wa 'yan Najeriya alkawari yayin yakin neman zabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel