Lokacin bai dace ba: Atiku ya nuna rashin amincewarsa ga ƙarin farashin lantarki

Lokacin bai dace ba: Atiku ya nuna rashin amincewarsa ga ƙarin farashin lantarki

- Jigo a PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya nuna rashin goyon bayansa da ƙarin farashin wutar lantarki

- Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da aiwatar da sabon farashin wutar lantarkin da zai fara aiki daga watan Agusta

- Atiku ya ce an yi ƙarin ne a lokacin da bai dace ba duba da cewa annobar korona ta lalata tattalin arzikin mutane

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya nuna rashin amincewarsa game da ƙarin kuɗin wutan lantarki a ƙasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da fara aiwatar da sabon tsarin farashin wutar lantarki, NESI, daga watan Agustan wannan shekarar.

Ana sa ran za a riƙa bitar sabon farashin wutar lantarkin duk bayan watanni hudu.

Tsarin ya bayar da damar yi wa kwastomomi masu hannu da shuni karin kuɗin lantarki domin a tsawaita lokutan da za su rika samun wuta da kuma ba su wuta mai ƙarfi.

The Cable ta ruwaito cewa, karin kuɗin wutar lantarkin ba zai shafi unguwanni da ake yi wa laƙabi da na 'talakawa' ba da wadanda ba su da mita.

Da ya ke tsokaci a kan batun Atiku ya ce ƙarin rashin ko in kula ne da halin da mutane ke ciki sakamakon annobar COVID-19.

Lokacin bai dace ba: Atiku ya nuna rashin amincewarsa ga ƙarin farashin lantarki
Lokacin bai dace ba: Atiku ya nuna rashin amincewarsa ga ƙarin farashin lantarki. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama mata biyu masu fashi da makami

Ya ce anyi ƙarin ne a "lokacin da bai dace ba" kuma ya ƙara da cewa a maimakon kari sauƙi ya kamata a ce an yi wa ƴan Najeriya.

"Ban amince da ƙarin kuɗin wutan lantarki ba a lokacin da ƴan Najeriya ke fitowa daga kulle, tallafi ƴan Najeriya ke bukata ba rashin tausayawa halin da suke ciki ba," kamar yadda Atiku ya rubuta a shafinsa na Twitter.

"Ƴan Najeriya da dama ba su samu albashi ba na tsawon watanni masu yawa kuma ba laifin su bane. Wannan ƙarin anyi shi ne a lokacin da bai dace ba."

Hukumar Tallata Albarkatun Man Fetur, PPMC, ita ce ta yi karin farashin litan man fetur daga N138.62 zuwa N151.56 a ranar Laraba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel