Hukumar Hisbah ta damke masu luwadi 2 a jihar Jigawa

Hukumar Hisbah ta damke masu luwadi 2 a jihar Jigawa

Hukumar Hisbah a jihar Jigawa ta damke wasu matasa biyu da ake zargi da laifin Luwadi a karamar hukumar Dutse.

Kwamandan hukumar Hisban jihar, Malam Ibrahim Dahiru, ya bayyana hakan yayinda yake hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ranar Laraba.

Ya ce an damke matasan biyu. masu shekaru 32 da 20, a wani dakin Otal dake Dutse, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi bayanin cewa wasu makwabta suka kawo musu kara yayinda suka ji hayaniyansu suna rikici kan kudi.

"Yau 2 ga Satumba, jami'anmu sun samu nasarar damke wasu mutane biyu da ake zargi da aikata luwadi a garin Dutse."

"Wani matashi mai shekara 32, Adamu, mazaunin Unguwa Uku a Jihar Kano, ya gayyaci tsohon abokinsa mai shekara 20, Tijjani, mazauni Garkuwar Sarki a jihar Sokoto."

"Sun hadu ne ta shafin Facebook, inda Tijjani ya garzayo Jigawa kan yarjejeniyar cewa za'a biya N50,000 bayan aikata aika-aikan."

"Sun shiga dakin Otal kuma suka kwana tare," Dahiru ya laburta.

"Adamu ya gaza biyan N50,000 din da ya yiwa bakonsa alkawari. Haka suka fara hayaniya har jama'a suka ji su kuma suka sanar da jami'anmu inda muka garzaya wajen muka damkesu."

Dahiru ya ce sun amince da aikata hakan kuma an garzaya da su ofishin yan sanda domin bincike da hukuntasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel