Mahaifi ya ajiye yaronsa cikin kejin kaji na tsawon shekaru 4 a Katsina

Mahaifi ya ajiye yaronsa cikin kejin kaji na tsawon shekaru 4 a Katsina

Wani mahaifi, Mallam Salisu Daura, ya ajiye dansa mai shekaru 16 da haihuwa, Sadiqu Daura, cikin keji na tsawon shekaru hudu saboda halin nakasa da yaron ke ciki.

Mahaifin ya tabbatar da haka ga mambobin wata kungiya mai zaman kanta, Save the Children, da suka ziyarci gidansa dake Daura, jihar Katsina ranar Talata, The Punch ta ruwaito.

Salisu ya bayyanawa mambobin kungiyar cewa: "Na yi nadamar abinda nayi kuma ba zan sake ba. Wadanda suka shigar dani kara ba makiya na bane...Yanzu na gane kura-kurai na."

"Ba ni da isasshen dakuna a gidana kamar yadda kuke gani. Ban jefashi cikin keji don in azabtar da shi ba ko don ban sonsa. Kawai na bashi wajen kamar daki ne."

Salisu Daura ya baiwa yaron sabon daki yanzu kuma an kusa a kammala ginin.

Bincike ya nuna cewa rayuwar Sadiqu ta fara fuskantar matsala ne lokacin da mahaifiyarsa ta rasu shekaru shida da suka gabata.

A matsayinsa mai nakasa, an kai shi gidan kakarsa, wacce kuma ta rasu daga baya.

Sai aka dawo da Sadiqu gidan mahaifinsa kuma ya ajiyesa a cikin keji.

Mahaifi ya ajiye yaronsa cikin kejin kaji na tsawon shekaru 4 a Katsina
Mahaifi ya ajiye yaronsa cikin kejin kaji na tsawon shekaru 4 a Katsina
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mawakin da yayi batanci ha Annabi ya daukaka kara

A wani labari mai alaka, Jami'an yan sanda a jihar Kano sun ceto wani matashi mai shekaru 32, Ahmad Aliyu, wanda mahaifinsa da kishiyar mahaifiyarsa suka kulle tsawon shekaru bakwai a jihar Kano.

Yan sandan sun kai wannan farmaki ne daren Litinin a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Mutumin, wanda hoto da bidiyo suka nuna yana cikin mawuyacin hali ya kwashe kwanaki babu abinci, babu ruwan sha sai dai shan fitsarinsa, HumAngle ta ruwaito.

Wata majiya ta bayyanawa HumAngle cewa mahaifinsa da kishiyar babarsa sun daureshi ne zargin cewa ya fara shaye-shaye da ta'amuni da kwayoyi.

Wata mata mai suna Rahama dake zama a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters, ta kaiwa yan sanda rahoto a Farawa kuma kungiyar rajin kare hakkin dan Adam suka garzayo cetonsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel