'Yan sanda sun kama mata biyu masu fashi da makami

'Yan sanda sun kama mata biyu masu fashi da makami

Rundunar ƴan sandan jihar Abia a ranar Laraba ta ce jami'anta sun kama wasu mata biyu da ake zargi da fashi da wasu 41 ciki har da mace mai safarar yara.

Rundunar ta ce an kama wadanda ake zargin ne cikin makonni shida da suka gabata.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Janet Agbede ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya ce baya da mata uku da aka kama kan zargin fashi da makami, an kama wasu mata ukun da ake zargi da satar yara da wasu maza 40 da ake zargi da wasu laifukan da suka hada da fashi, garkuwa da shiga ƙungiyar asiri.

'Yan sanda sun kama mata biyu masu fashi da makami
'Yan sanda sun kama mata biyu masu fashi da makami
Asali: Twitter

Agbede ya ce cikin wadanda aka kama ɗin, biyu daga cikin su masu kashe mutane ne, gudu uku masu garkuwa, yan fashi bakwai, masu safarar mutane bakwai sauran kuma ƴan kungiyar asiri.

Kwamishinan ya ce ƴan fashi matan da aka kama sun ƙware wurin fashin ne tare da abokan aikinsu maza da ke yi wa masu achaɓa fashi.

Ya ce matan kan hau babur sai idan ɗan achaɓa ya kai su inda za su sauka kwatsam sai mazan su fito da bindigu su yi wa ƴan achaɓan nasu fashi.

Agbede ya ce wani Sunday Okoro mazaunin Ubahu, Okogwe daga jihar Imo ya gane wasu daga cikin wadanda ake zargin da ya ce sun masa fashin babur ɗinsa.

Kwamishinan ya kuma ce wata da ake zargi da safarar yara, Iheci Ogbonna mai shekaru 22 daga Ohanze a ƙaramar hukumar Ogingwa a ranar 18 ga watan Agusta ta shiga gidan wani Benjamin Christopher a Amaukwu, Umuahia ta saka kayan matarsa.

Hakan yasa yaran Christopher maza biyu suka yi tsamannin mahaifiyarsu ce kuma suka bi ta a lokacin da ta bukaci hakan.

Wacce ake zargin tana tafiya da yaran a unguwa amma wasu matasa suka tsare ta suka sanar da ƴan sanda daga Ubakala sannan aka ceto yaran.

Wacce ake zargin ta amsa laifin ta kuma a halin yanzu ana ƙoƙarin gano wadanda suke satar yaran tare a cewar ƴan sandan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164