Boko Haram sun kai wa 'yan gudun hijira hari, sun yi garkuwa da mutum 4

Boko Haram sun kai wa 'yan gudun hijira hari, sun yi garkuwa da mutum 4

A kalla mutum hudu cikin 'yan gudun hijira mayakan Boko haram suka yi awon gaba da su a yayin da suke gonakinsu a kusa da Maiduguri a ranar Talata, wasu majiyoyi suka tabbatar.

An gano cewa, mayakan Boko Haram sun kutsa Dalwa da ke kusa da yankin Molai a Maiduguri da ke jihar Borno. Sun kai wa manoman hari tare da yin awon gaba da hudu daga ciki.

Ganau ba jiyau ba da suka bada labari, sun ce mayakan ta'addancin sun kai harin a kan babura ga manoman da basu da mataimaka.

Mallam Babagana, wanda ya sha da kyar daga harin 'yan ta'addan ya ce a kan idonsa aka kwashe mutane hudun.

Da kanshi ya bayyana wa iyalan wadanda lamarin ya shafa. Hakan kuwa ya janyo tashin hankali a sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi.

"A yau, daya ga watan Satumban 2020, wurin karfe 4:20 na yammaci mayakan Boko Haram suka kutsa gonakin 'yan gudun hijira da ke Dalwa a Molai suka yi awon gaba da mutane hudu," yace.

Majiyoyin sun kara da cewa, "Daga cikin wadanda suka tsere akwai Mallam Babagana wanda ya dawo sansanin ya sanar da yadda lamarin ya faru.

"Ya bayyana cewa mayakan Boko Haram sun iskesu a gonakinsu inda suka kama mutum hudu suka yi hanyar dajin Sambisa da su.

"Wannan lamarin ya mtukar tada hankalin jama'a mazauna sansanin 'yan gudun hijirar."

Boko Haram sun kai wa 'yan gudun hijira hari, sun yi garkuwa da mutum 4
Boko Haram sun kai wa 'yan gudun hijira hari, sun yi garkuwa da mutum 4. Hoto daga HumAngle
Source: UGC

KU KARANTA: Mun sha matukar azaba - Iyalan Abiola sun bayyana arangamarsu da 'yan bindiga

A wani labari na daban, jsojojin saman Najeriya sun tarwatsa wasu gine-gine na ƴan ta'addan kungiyar Islamic State of West African Province (ISWAP) a Kaza da ke Gulumba-Gana a jihar Borno.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole, Manjo Janar John Enenche ne ya sanar da hakan ta shafin twitter na rundunar tsaro.

Ya ce sai da aka samu bayanan sirri sahihai da ke tabbatar da ƴan ta'addan na cikin gine ginen kafin aka kai harin.

Wani sashi na cikin sanarwar ta ce, "a ƙoƙarin cigaba da yaƙi da miyagu a yankin Arewa maso gabashin kasar, dakarun saman Operation Lafiya Dole sun kashe wasu ƴan ta'addan kungiyar ISWAP suka kuma lalata sansanin su a Kaza kan hanyar Galumba Gana-Kumshe a jihar Borno.

"An kai harin saman ne a ranar 1 ga watan Satumba bayan samun bayanan sirri masu inganci daga mutane da kuma amfani da na'urar leƙen asiri ta ISR da ya nuna akwai ƴan ta'addan suna harkokin su a wurin.

"Luguden wutan da jiragen yaƙin mu da jirag masu saukan ungulu suka yi ya yi sanadiyar lalata sansanin tare da kashe wasu mayakan kungiyar ta ISWAP."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel