Tashin hankali: Gwanda ku kasheni da ku raba ni da gonar wiwi na - Cewar wani mai gonar wiwi da NDLEA suka kama

Tashin hankali: Gwanda ku kasheni da ku raba ni da gonar wiwi na - Cewar wani mai gonar wiwi da NDLEA suka kama

- Wani mutumi da aka kama a jihar Kogi da katuwar gona ta wiwi

- Ya bukaci jami'an hukumar NDLEA da su dauki rayuwarshi akan su lalata mishi gona

- Ya ce baya son shiga fashi da makami ko satar mutane ne yasa ya fara wannan sana'a

Wani mutumi mai shekaru 42 da aka bayyana sunanshi da Clement Akor, jami'an hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi sun kama shi a jihar Kogi, inda ya dinga rokon su akan su dauki rayuwarshi da su bata masa gonarshi mai girman kadada 10 wacce ya shuka tabar wiwi a ciki.

Mutumin wanda ke da 'ya'ya guda shida, an kama shi tare da abokinsa David Ameh a kauyen Enabo dake cikin karamar hukumar Ankpa jihar Kogi, ya bayyana cewa ya kashe kudi da yawa a gonarshi.

Tashin hankali: Gwanda ku kasheni da ku raba ni da gonar wiwi na - Cewar wani mai gonar wiwi da NDLEA suka kama
Tashin hankali: Gwanda ku kasheni da ku raba ni da gonar wiwi na - Cewar wani mai gonar wiwi da NDLEA suka kama
Source: Facebook

Ya ce yana da masaniya kwarai da gaske akan dokar sayar da tabar wiwi, Akor ya ce:

"Ni ne mai wannan gonar. Na koyi nomanta a yankin Yarabawa. Dana girbe a shekarar da ta gabata an sace mini. To wannan shekarar sai na siyo iri daga can yankin na Yarabawa na shuka sabuwa.

'Irin wannan sana'ar sa'a ce. A wannan gonar zan iya samun buhunhuna da yawa. Nan da mako biyu ya kamata nayi girbi. Yanzu kuma kunzo zaku lalata mini gona. Kawai ku kashe ni, domin ba zan iya zuba ido ina gani ku lalata mini gona ba wacce na wahala na kashe kudi a kanta. Ina neman kudine saboda ni banyi karatu ba. Ban so na shiga harkar fashi da makami haka ya sanya na shigo wannan sana'ar."

KU KARANTA: Babu ranar fita: An yankewa jarumin da yake yin fim din batsa hukuncin shekaru 250 a gidan yari

Tashin hankali: Gwanda ku kasheni da ku raba ni da gonar wiwi na - Cewar wani mai gonar wiwi da NDLEA suka kama
Tashin hankali: Gwanda ku kasheni da ku raba ni da gonar wiwi na - Cewar wani mai gonar wiwi da NDLEA suka kama
Source: Facebook

Kwamandan rundunar ta NDLEA, Alfred Adewumi, ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, haka kuma ya bayyana cewa an kama su bayan samun bayanan sirri da suka yi.

Shugaban na hukumar ya bayyana cewa za su mika duka masu laifin gaban kotu da zarar sun kammala binciken da suke yi a kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel