Akwai yiwuwar ƴan ta'adda za su koma neman mambobi ta hanyar yanar gizo - Buhari

Akwai yiwuwar ƴan ta'adda za su koma neman mambobi ta hanyar yanar gizo - Buhari

- Shugaba Buhari ya nuna damuwarsa kan yiwuwar ƴan ta'adda su rika gurɓata tunanin mutane ta yanar gizo

- Shugaban ya yi wannan jawabin ne yayin taron AQABA da aka gudanar a Jordan ta yanar gizo

- Buhari ya ce kulle da taƙaita zirga zirga ya saka an koma yin harkoki ta intanet kuma miyagu suma za su yi amfani da wannan damar

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya nuna fargabarsa kan yiwuwar yan ta'adda su koma neman mambobi ta hanyar amfani da intanet saboda dokar kulle da aka saka sakamakon korona.

Ya ce saboda haka gwamnati za ta fara sanya idanu a kan ƴan ta'adda a yanar gizo domin kare mutane daga faɗawa tarkonsu.

Akwai yiwuwar ƴan ta'adda za su koma neman mambobi ta hanyar yanar gizo - Buhari
Akwai yiwuwar ƴan ta'adda za su koma neman mambobi ta hanyar yanar gizo - Buhari
Source: Twitter

A cewar sanarwar da kakakinsa, Femi Adesina ya fitar, shugaban ƙasar ya furta hakan ne yayin jawabin sa a taron AQABA da aka yi ta intanet a masarautar Jordan.

An yiwa sanarwar laƙabi da, 'A yayin taron intanet ta AQABA, Shugaba Buhari ya yi magana kan alaka tsakanin COVID-19 da tsaro.'

Adesina ya ruwaito cewa shugaban ƙasa ya ce komawa amfani da intanet ya haifar da ƙaluballe game da gurɓata tunanin mutane musamman saboda takaita yawo da cudanya.

DUBA WANNAN: Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu

"Yana da muhimmanci a bayyana cewa yaɗuwar COVID 19 ya saka an koma gudanar da abubuwa ta intanet.

"Kazalika, dokar kulle da taƙaita zirga zirga na nufin mutane za su koma gudanar da harkokinsu a yanar gizo.

"Sai da hakan ya kawo ƙaruwar hatsarin yiwuwar gurɓata tunanin mutane a yanar gizon," in ji sanarwar.

Amma Buhari ya ce gwamnatin tarayya za ta cigaba da ɗaukan matakai da suka dace da sabon yanayin tare da mayar da hankali kan tsaro a yayin da masana ke kokarin neman riga kafi ko maganin Covid 19.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel