Da duminsa: Yan bindiga na can suna cin karensu ba babbaka a Kagara, jihar Niger
Rahotannin da muke samu daga gidan talabijin na AIT, na nuni da cewa 'yan bindiga sun kai farmaki a garin Kagara, shelkwatar karamar hukumar Rafi, jihar Niger. An ruwaito cewa 'yan bindigar sun farmaki wani banki a cikin garin.
Ita kuwa jaridar The Nation, ta ruwaito cewa akalla 'yan bindiga 70 ne haye a saman babura suka mamaye garin, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
A yayin da wata majiya da ta yiwa wakilin jaridar kiran gaggawa, don shaida masa abunda ke faruwa, wakilin ya ce yana iya jiyo karar harbe harben bindiga.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa da yawa daga cikin mazauna garin sun gudu sun bar gidajensu, tare da buya a cikin gonaki, don tsira da rayukansu.
Sai dai duk wani kokari na tuntubar jami'in hulda da jami'in tsaro na rundunar 'yan sandan jihar, ASP Wasiu Abiodun don jin ta bakinsa kan harin ya ci tura.
Cikakken labarin yana zuwa...
KARANTA WANNAN: Ko gwamnati ta bayar da umurni, mu ba zamu bude makarantu ba - Kungiyar malamai

Asali: Facebook
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng