Katsina: Ƴan banga sun fafata da ƴan bindiga, mutum biyu sun mutu

Katsina: Ƴan banga sun fafata da ƴan bindiga, mutum biyu sun mutu

An kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne a lokacin da ƴan banga a ƙauyen Yantara da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a Katsina suka yi fito na fito da ƴan bindiga da suka kai hari ƙauyen ranar Talata.

Wani mutum mai suna Mamman Dahiru mai shekaru 30 a duniya shima ya rasa ransa sakamakon harin.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Laraba.

Katsina: Ƴan banga sun fafata da ƴan bindiga, mutum biyu sun mutu
Katsina: Ƴan banga sun fafata da ƴan bindiga, mutum biyu sun mutu
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu

An gano cewa ƴan bindigan sun kai farmaki ƙauyen ne a misalin ƙarfe ɗaya na daren ranar Talata.

The Punch ta ruwaito cewa sun yi wa mutane rauni, sun yi fashi a gidaje sannan sun sace dabbobi.

Ƴan bangar sun yi wa ƴan bindigan kwantar ɓauna ne suka faɗa musu a hakan ne mutum biyu suka rasa rayukansu.

Kakakin ƴan sandan ya ce, "Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 1 na daren ranar Talata. Yan bindigan sun kai hari ƙauyen Yantara kuma ƴan bangan suka kashe ɗan bindiga ɗaya yayin da wani Mamman Dahiru mazaunin ƙauyen shima ya rasu."

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji wasu mutane dauke da bindigu da har yanzu ba a san ko su wanene ba sun afka gidan Moshood Abiola da ke Ikeja a Legas.

Yan fashin sun sace kudade masu yawa na ƙasashe daban-daban da a halin yanzu ba a tabbatar da adadin su ba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A lokacin da ake hada wannan rahoton, jami'an tsaro sun kama mutum bakwai (7) sun kuma mika su hannun ƴan sandan SARS.

Masu gadin gidan sun ki yin magana da majiyar Legit.ng amma wasu yan unguwa da abin ya faru a gabansu sun ce yan bindigan sun kutsa cikin gidan ne ta baya yayin da masu tsaron gidan ke barci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel