Jiragen yaƙin NAF sun tarwatsa sansanin ƴan ISWAP a Kaza (Bidiyo)

Jiragen yaƙin NAF sun tarwatsa sansanin ƴan ISWAP a Kaza (Bidiyo)

Jiragen sojojin saman Najeriya sun tarwatsa wasu gine-gine na ƴan ta'addan kungiyar Islamic State of West African Province (ISWAP) a Kaza da ke Gulumba-Gana a jihar Borno.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole, Manjo Janar John Enenche ne ya sanar da hakan ta shafin twitter na rundunar tsaro.

Ya ce sai da aka samu bayanan sirri sahihai da ke tabbatar da ƴan ta'addan na cikin gine ginen kafin aka kai harin.

Jiragen yaƙin NAF sun tarwatsa sansanin ƴan ISWAP a Kaza (Bidiyo)
Jiragen yaƙin NAF sun tarwatsa sansanin ƴan ISWAP a Kaza (Bidiyo)
Source: Facebook

Wani sashi na cikin sanarwar ta ce, "a ƙoƙarin cigaba da yaƙi da miyagu a yankin Arewa maso gabashin kasar, dakarun saman Operation Lafiya Dole sun kashe wasu ƴan ta'addan kungiyar ISWAP suka kuma lalata sansanin su a Kaza kan hanyar Galumba Gana-Kumshe a jihar Borno.

DUBA WANNAN: Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu

"An kai harin saman ne a ranar 1 ga watan Satumba bayan samun bayanan sirri masu inganci daga mutane da kuma amfani da na'urar leƙen asiri ta ISR da ya nuna akwai ƴan ta'addan suna harkokin su a wurin.

"Luguden wutan da jiragen yaƙin mu da jirag masu saukan ungulu suka yi ya yi sanadiyar lalata sansanin tare da kashe wasu mayakan kungiyar ta ISWAP."

Ga bidiyon a kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel