Karya ne, hadimi mafi kusa da Buhari bai kamu da Korona ba - Fadar shugaban kasa

Karya ne, hadimi mafi kusa da Buhari bai kamu da Korona ba - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta karya rahoton cewa babban hadimin shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin cikin gidansa, Sarki Abba, ya kamu da muguwar cutar nan ta Korona.

Sarki Abba, shine hadimin da ya fi kusa da shugaba Buhari saboda sun kwashe shekaru daya suna tare.

A jawabi daga fadar shugaban kasa a ranar Laraba, Garba Shehu, mai magana da yawun Buhari, ya ce labarin ba gaskiya bane, Abba bai kamu da Korona ba.

Garba Shehu ya ce dukkan mutanen da ke zagaye da Buhari na gwajin cutar Korona akai-akai domin tabbatar da lafiyan shugaban kasa.

Ya ce Abba bai taba kamuwa da cutar ba.

Karya ne, hadimi mafi kusa da Buhari ba kamu da Korona ba - Fadr shugaban kasa
Karya ne, hadimi mafi kusa da Buhari ba kamu da Korona ba - Fadr shugaban kasa
Asali: Twitter

"Fadar shugaban kasa na son baiwa yan Najeriya shawara suyi watsi da dillalan yada labaran karya wa jama'a." Garba Shehu yace

"Muna martani kan karerayi da labaran bogin da wata jaridar zamani keyi cewa hadimin shugaba Muhammadu Buhari, Sarki Abba ya kamu da cutar COVID-19."

"Wannan rahoto karya ne kuma jaridar na son batar da al'umma."

"Bisa umurnin likitoci da masana ilmin kimiya da kuma luran shugaban ma'aikata, Farfesa Ibrahim Gambari, dukkan ma'aikata da na kusa da Buhari na gwaji akai-akai na cutar."

"Hadimin Buhari kan harkokin cikin gidansa, Sarki Abba, bai taba kamuwa ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel