Uwar saurayi da kannansa sun tilasta budurwar wanke kwalliyarta daga zuwa gaisuwa

Uwar saurayi da kannansa sun tilasta budurwar wanke kwalliyarta daga zuwa gaisuwa

- Wata wallafar wani matashi a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ta janyo cece-kuce daga samari da 'yan mata

- Wani matashi mai suna Donald ya wallafa wani labari inda saurayi ya kai wa danginsa budurwar da yake son aure a Ibadan

- Ganin fuskar budurwa da kwalliya, mahaifiyar saurayin da kanninsa mata sun bukaci ta wanke kwalliyar domin su tantance asalin fuskarta

Wani ma'abocin amfani da Twitter ya yi wani bayani wanda ya janyo cece-kuce a kafar.

Ya bayyana yadda mahaifiyar saurayi da 'yan uwansa suka bukaci budurwar da ya kai musu, da ta wanke kwalliyarta a ziyarar farko da ta kai musu.

Donald ya ce, masu niyyar zama sirikan sun ce suna son ta goge kwalliyarta ne domin su ga fuskarta sosai.

Hakan ne yasa suka mika mata tsumma domin ta goge kwalliyarta, amma budurwar ta ki yin hakan.

Ya wallafa: "Wani matashi ya kai wa mahaifiyarsa da danginsa budurwarsa a garin Ibadan. Mahaifiyarsa da 'yan uwansa mata sun bukaci da ta wanke fuskarta ta yadda za su kalleta da kyau.

"Bata amince da wanan lamarin ba, hakan yasa suka mika mata tsumma domin ta goge fuskarta amma ta ki."

Wannan wallafar ta janyo cece-kuce domin kuwa wasu sun kalla hakan a matsayin cin mutunci da cin zarafi.

Uwar saurayi da kannansa sun tilasta budurwar wanke kwalliyarta daga zuwa gaisuwa
Uwar saurayi da kannansa sun tilasta budurwar wanke kwalliyarta daga zuwa gaisuwa. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Fitacciyar jaruma Maryam AB Yola ta fita daga Kannywood, ta sanar da daina fitowa a fim

Wasu daga cikin martanin da samari da 'yan mata suka dinga yi wa wannan wallafar ta hada da:

Uwar saurayi da kannansa sun tilasta budurwar wanke kwalliyarta daga zuwa gaisuwa
Uwar saurayi da kannansa sun tilasta budurwar wanke kwalliyarta daga zuwa gaisuwa. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Source: Twitter

Uwar saurayi da kannansa sun tilasta budurwar wanke kwalliyarta daga zuwa gaisuwa
Uwar saurayi da kannansa sun tilasta budurwar wanke kwalliyarta daga zuwa gaisuwa. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Source: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel