An kama wani da ya dauki dan uwansa aiki ba bisa ka'ida ba a Niger
- An kama wani mutum da ke aiki a ma'aikatar lafiya ta jihar Niger da ya ɗauki ɗan uwansa aiki ba bisa ka'ida ba
- Kwamishinan ƴan sandan jihar ya ce kwamitin tantance ma'aikata ta gano badaƙalar ne yayin aikinta
- An gano cewa mutum ya ɗauki ɗan uwansa aikin ne tun a 2009 a kan mataki na 11 duk da bashi da takardu yanzu har ya kai mataki na 14
Ƴan Sanda a jihar Niger sun kama yaya da ƙani da ake zargi da hannu cikin damfarar daukan aiki a ma'aikatar lafiya ta jihar.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Mista Adamu Usman ya shaidawa manema labarai a Minna a ranar Talata cewa an gano badaƙalar ne yayin aikin tantance ma'aikata a jihar.

Asali: Twitter
Ya ce kwamitin binciken ta gano cewa wani ma'aikacin hukumar ya saka sunan ɗan uwansa a jerin sunayen waɗanda gwamnatin jihar zata ɗauka aiki a jihar.
A cewar kwamishinan ƴan sandan, an gano cewa an ɗauki daya daga cikin ƴan uwan aiki a gwamnatin jihar a matsayi ta 11 ba tare da ya mallaki takardun da ake bukata ba.
DUBA WANNAN: Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu
Usman ya ce kwamitin ta gano wani daga cikin ma'aikacin ta a ma'aikatar lafiya ya ɗauki ɗan uwansa mai sana'ar achaɓa aiki ba tare da ya mallaki takardun da suka cancanta ba tun a 2009.
"Mohammed Ndanusa ya amsa cewa ya aikata laifin inda ya ce ya ɗauki ɗan uwansa aiki a mataki ta 11 a 2009 kuma ya yi ta yi masa ƙarin girma zuwa matakinsa na yanzu na 14"
Kwamishinan ƴan sandan ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng