An kama matar da ta sanya wuta ta konewa 'yar akinta gaba akan ta daukar mata abinci

An kama matar da ta sanya wuta ta konewa 'yar akinta gaba akan ta daukar mata abinci

- An kama matar da ta yi amfani da wuta ta kone gaban 'yar aikinta

- Matar dai ta sanya diyarta da wata 'yar aikine suka rike mata yarinyar

- Tayi amfani da ashana ta kone gaban yarinyar da mazaunanta

Wata kotun majistire dake a Gabasawa kan titin Taiwo Road, dake Kaduna, ta bada umarnin sanya Mrs. Yemi Awolola, wacce ta azabtar da 'yar aikinta mai shekaru 14 mai suna Princess Michael, da a kaita gidan gyaran hali har zuwa ranar 10 ga watan Satumbar, 2020, inda daga nan za a mikawa babbar kotu shari'ar.

Kotun majistiren dake a Gabasawar, a ranar 13 ga watan Yuli, ta daga sauraron karar da ake zargin Mrs Awolola da shi, mai lamba: KMD/204XB/2020, zuwa ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata.

An kama matar da ta sanya wuta ta konewa 'yar akinta gaba akan ta daukar mata abinci
An kama matar da ta sanya wuta ta konewa 'yar akinta gaba akan ta daukar mata abinci
Source: UGC

Alkalin kotun Majistiren, Benjamin Hassan, bayan karanta wannan kara ga wadanda ake zargin duka cikin harshen Turanci da Hausa, ya bayyana cewa sakamakon dangantaka da sashi na 207 na kundin tsarin mulkin kasa, akan shari'ar, iya babbar kotu ce kawai za ta iya yanke hukunci akan wannan shari'a.

Ya ce: "Karar yanzu na gaban kotun majistire, saboda kotun majistire ta farko ta kawo shari'ar zuwa wata kotun.

KU KARANTA: Babu ranar fita: An yankewa jarumin da yake yin fim din batsa hukuncin shekaru 250 a gidan yari

"Sabuwar kotun ta yanzu ta bawa yara biyu dake da dangantaka da wannan lamari beli saboda yarane kanana, da kuma ikirarin da cibiyar gyaran hali tayi na cewa bata da wajen da za ta ajiye yaran.

Da take martani game da wannan lamari, darakta ta cibiyar kawo mafita ga cin zarafin al'umma, Farfesa Hauwau Evyn Yusuf, ta ce dole ne ayi hukunci akan wannan lamari.

"Tunda na shigo cikin wannan lamari, babban abinda nake sa ran za ayi shine adalci.

"Muna so muga duka hukuncin da za a yanke domin tabbatar da cewa ana yin abinda ya kamata.

A ranar 3 ga watan Yuli ne dai, Mrs Yemi Awolola, ta sanya diyarta (karamar yarinya) da kuma wata 'yar aiki (ita ma yarinyar), suka rike mata kafafuwan Princess Michael; wacce ke da shekaru 14 kacal, tayi amfani da ashana ta kona mata gaba da mazaunanta, saboda tana zargin ta daukar mata kayan abinci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel