Shekarata 20 ina aikin N700 a rana, amma hakan yafi mini rufin asiri da naje nayi sata - Cewar Lebura
- Wani mutumi dan Najeriya mai suna Emmanuel Menuwa, ya ce yana samun N700 ne a kowacce rana fiye da shekara 20 da suka wuce a matsayin lebura
- Saurayin yace ya zabi zama lebura ne saboda baya so ya fada harkar sata
- A cewar saurayin mai shekaru 36, yana da da mai shekaru 13 a duniya
Wani mutumi mai shekaru 36, mai suna Emmanuel Menuwa, ya bayyana cewa yana samun N700 ne a kowacce rana fiye da shekaru 20 da suka gabata a matsayin lebura.
Da yake hira da Legit TV, Emmanuel, wanda yake aiki a Ogbe-Ijoh Jetty dake Warri, cikin jihar Delta, ya ce yana yin wannan aikin karfine saboda bashi da wani abu da zai yi kuma baya so yayi sata.
Emmanuel, wanda ya dakata da karatun shi tun yana matakin farko na makarantar sakandare, yana taimakawa wacce ke sayar da kifi yana tura mata tana sayarwa da mutane a titi.
Mutumin wanda yake da yaro dan shekara 13, ya ce da tuni yanzu yayi nisa a aikin da yake mafarkin yi a rayuwar shi da ace ya samu damar cigaba da karatun shi.
KU KARANTA: Rikici ya barke a wajen biki, bayan 'yan uwan miji sun gano cewa amaryar da zai aura tana da miji
Bayan wallafa wannan bidiyo a shafin Legit TV na YouTube, mutane da yawa sun dinga tofa albarkacin bakinsu kan wannan rayuwa ta bawan Allan.
Wata mai suna Dianna Connors ta ce: "Kai mutum ne mai gaskiya, na san cewa aikin leburanci na da matukar wahala, saboda tsohon mijina yayi irin wannan aikin a kasar Ingila (tun lokacin da ya zo daga Ireland a shekarar 1960), kwarai kuwa kudin da ya samu ya fi mishi sosai, amma kuma gajiyar dake jikin shi nada yawa...Allah yayi maka albarka, kuma Allah ne kadai yasan muhimmancin ka, sakamakon ka yana Aljanna."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng