An kama wani mutum da ya saci kifi ya boye su a ƙugunsa a wani babban kanti (Hotuna)
An kama wani mutum mai ƙananan shekaru da kifin gwangwani jere a ƙugunsa yayin da ya tafi yin siyayya a wani babban kanti.
Wani mai amfani da dandalin sada zumunta ta Facebook, Segun Aveileth Oyedele da ya wallafa labarin ya ce mutumin ya shiga kantin ne kamar ya tafi yin siyayya.
Amma daga bisani sai wani daga cikin masu sayar da kaya a kantin ya lura cewa akwai alamar wani matsala tattare da ƙugun mutumin kamar yadda LIB ya ruwaito.
Da aka tilasta masa ya ɗaga rigarsa sai aka gano ya yi ɗamara da kifin gwangwani har guda shida cikin gajeren wandonsa da nufin ya fice da su ya tafi ba tare da ya biya kudi ba.
Ga cikakken hotunan a ƙasa:

Asali: Facebook

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu

Asali: Facebook

Asali: Instagram
Ma'abota amfani da dandalin sada zumunta sun bayyana ra'ayoyin su game da lamarin inda wasu ke cewa yunwa ce ta saka ya aikata hakan kuma ayi masa afuwa wasu kuma na ganin rashin godiyar Allah ne da kwaɗayi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng