Dangote ya bukaci a bawa Okonjo Iweala babban mukami a WTO

Dangote ya bukaci a bawa Okonjo Iweala babban mukami a WTO

- Ngozi Okonjo-Iweala na ta samun goyon baya daga sassa daban-daban a kokarin da take na zama darakta janar a kamfanin kasuwanci na duniya

- Kwanan nan, tsohuwar ministar kudin ta Najeriya ta samu goyon bayan Aliko Dangote wajen samun wannan mukami

- Fitaccen dan kasuwar ya bayyana cewa WTO na bukatar Iweala a matsayin jigo wajen kasuwanci a duniya

Aliko Dangote, daya daga cikin manyan masu kudin nahiyar Africa, ya nuna goyon bayansa ga tsohuwar ministar kudi, Ngozi Okonjo-Iweala, a matsayin wacce ta dace ta rike mukamin darakta janar ta kamfanin kasuwanci na duniya.

Dangote ya bayyana cewa kamfanin na bukatar wacce keda kwarewa ta kowanne fanni na kasuwanci a duniya kamar Okonjo-Iweala a matsayin jagora.

Fitaccen mai kudin na Afrika ya nuna goyon bayansa ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 1 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Bude makarantu: Gwamnatin tarayya ta gargadi jihohin da suke shirin bude makarantu a Najeriya

Dangote ya ce: "A wannan lokaci da muke ciki, WTO tana bukatar mutum mai kwarewa kamar Dr Ngozi Okonjo Iweala ta jagoranci kamfanin a wannan lokaci da ake ta fama da matsaloli iri-iri.

"Na zabe ta a kowanne mataki. Ina goyon bayanta dari bisa dari ta jagoranci WTO."

Dangote ya bukaci a bawa Okonjo Iweala babban mukami a WTO
Dangote ya bukaci a bawa Okonjo Iweala babban mukami a WTO
Asali: UGC

Fitaccen dan yankin arewan ya bayyana cewa tunda har Okonjo Iweala ta gano matsalolin da ake samu a fannin kasuwanci na duniya, za ta iya kawo karshen duka matsalolin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel