Da duminsa: Shugaba Keita na kasar Mali yana kwance a asibiti, rai a hannun Allah

Da duminsa: Shugaba Keita na kasar Mali yana kwance a asibiti, rai a hannun Allah

Ibrahim Boubacar Keita, shugaban kasar Mali da sojoji suka yi wa juyin mulki a watan da ya gabata yana kwance a gadon asibiti, jaridar Vanguard ta ruwaito hakan.

A ranar Talata aka kwantar da dattijon mai shekaru 75 a wani asbiti mai zaman kansa, bayan fitowa da yayi daga hannun sojin juyin mulkin da suka tsaresa na tsawon kwanaki 10.

Jaridar Associated Press ce ta tabbatar da kwanciyarsa a asibitin bayan zantawa da tayi da mutum biyu daga asibitin da suka bukaci a boye sunansu.

Tsohon shugaban kasar Malin ya bayyana a rame a hotunansa na kwanakin nan bayan fitowarsa daga hannun soojin juyin mulkin, wadanda suka adana shi a wata bariki da ke wajen babban birnin kasar.

An fara zabar Keita a shekarar 2013, yana da ragowar shekaru 3 na mulkinsa kafin sojin juyin mulki su hambarar da gwamnatinsa.

Bayan sa'o'i kadan da sojin suka damkesa, ya bayyana a wani shirin kai tsaye na gidan talabijin yana bayyana cewa zai yi murabus domin gujewa zubar da jini.

Da duminsa: Shugaba Keita na kasar Mali yana kwance a asibiti, rai a hannun Allah
Da duminsa: Shugaba Keita na kasar Mali yana kwance a asibiti, rai a hannun Allah. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sa kai sun fatattaki masu garkuwa da mutane, sun kashe 3 a take

Dakarun sojin da suka kira kansu da kwamitin kasa na ceton jama'a, sun ce sun tsare Keita a wurinsu domin bashi kariya.

A zanga-zangar da dubban 'yan kasar suka yi wanda hakan ya kawo hambarar da gwamnatinsa, sojin sun ce alamu ya bayyana cewa ba zai sha da kyau daga hannun jama'a.

Babu kakkautawa ECOWAS ta fada lamarin tare da sanya wa kasar Mali takunkumi, ta rufe iyakokinta da su, tsayar da shiga da ficen kudi tsakaninsu tare da barazanar ladabtar da su.

ECOWAS ta tura kungiyar sasanci wacce tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya shugabanta domin ganawa da Keita a barikin sojin.

Daga bisani, wakilan ECOWAS sun sanar da manema labarai cewa Keita ya sanar da cewa ba ya bukatar komawa mulkin kasar Mali.

Kasar Faransa da majalisar dinkin duniya sun yi kira da a gaggauta sakin Keita, kuma an sakesa inda ya koma gidansa a ranar Alhamis da ta gabata inda sojin ke gadin lafiyarsa.

Wani dan uwan Keita ya sanar da cewa, Keita bai samu damar ganin likitansa ba.

Duk da sakinsa, ECOWAS ta ci gaba da matsawa sojin juyin mulkin da su gaggauta mika mulki ga farar hula, wanda suka amince za su yi hakan cikin shekara daya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel