Babu ranar fita: An yankewa jarumin da yake yin fim din batsa hukuncin shekaru 250 a gidan yari

Babu ranar fita: An yankewa jarumin da yake yin fim din batsa hukuncin shekaru 250 a gidan yari

- Wani jarumi da yake yin fim din batsa za a yanke masa hukuncin shekaru 250 a gidan yari

- An kama shi da laifin yiwa mata da yawa fyade ciki kuwa harda karamar yarinya

- Mutumin mai suna Ronald Jeremy Hyatt, dama can ya jima a gidan yari, inda aka bukaci ya biya belin $6.6m

An kama jarumin fim din batsa, Ron Jeremy, da laifuka guda ashirin da suke da hadi da cin zarafin mata 12 da kuma yarinya karama, da aka gano tun a shekarar 2004, cewar ofishin alkalin-alkalai na Los Angeles.

Mutumin wanda yake da shekaru 67, da ainahin sunansa yake Ronald Jeremy Hyatt, an kama shi da laifuka a watan Yuni da suka hada da fyade guda uku. Haka kuma ya amsa laifinsa.

Babu ranar fita: An yankewa jarumin da yake yin fim din batsa hukuncin shekaru 250 a gidan yari
Babu ranar fita: An yankewa jarumin da yake yin fim din batsa hukuncin shekaru 250 a gidan yari
Source: Facebook

A ranar Litinin ne 31 ga watan Agusta, aka sake gano wasu laifuka guda 20 da Jeremy ya aikata, inda aka bayyana cewa ya yiwa mata 13 fyade tun a shekarar 2004.

An kama Jeremy dai ya yiwa wata yarinya 'yar shekara 15 fyade a lokacin da take bacci, inda ya sanya mata wani abu a gabanta.

An ce Jeremy ya yiwa yarinyar fyade ne a shekarar 2004, haka kuma ana zargin shi da yiwa wata mata fyade a cikin wannan shekarar.

KU KARANTA: Rikici ya barke a wajen biki, bayan 'yan uwan miji sun gano cewa amaryar da zai aura tana da miji

An bukaci Jeremy ya dawo kotu a cikin watan Oktoba. Idan aka same shi da duka laifukan da ake zargin shi dasu, za a yanke masa hukuncin shekaru 250 a gidan yari.

A yadda wani rahoto na yanar gizo ya bayyana, tuni dama Jeremy yana gidan yari a Los Angeles, inda ake tsare dashi tare da sanya belin dala miliyan shida da dubu dari shida ($6.6m).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel