Kutse a gonar Obasanjo: An gurfanar da dattijo mai shekaru 60

Kutse a gonar Obasanjo: An gurfanar da dattijo mai shekaru 60

An gurfanar da wani mutum mai shekaru 60, Ibrahim Ibuoye a gaban kotu bisa zarginsa da kutse cikin gonar tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da ke Ota.

An gurfanar da Ibuoye ne a kotun majistare da ke zamanta a Ado Odo a ƙaramar hukumar Ota ta jihar Ogun.

An gurfanar da Ibuoye, wanda ba shi da takamaiman adireshi kan laifuka hudu da suka hada da tayar da zaune tsaye, kutse, barna da hadin baki.

Kutse a gonar Obasanjo: An gurfanar da dattijo mai shekaru 60
Kutse a gonar Obasanjo: An gurfanar da dattijo mai shekaru 60
Source: UGC

Amma wanda ake zargin bai amsa laifin ba.

KU KARANTA: Matawalle ya bawa malamin Zamfara muƙami bayan karɓo shi daga gidan yari a Saudiyya

Ɗan sanda mai shigar da ƙara, Sufeta Rosemary Samson, ta shaida wa kotu wanda ake zargin da wasu da ake nema sun aikata laifin ne a ranar 26 ga watan Agusta a Obasanjo Farms Limited da ke Ota.

Samson ta ce wanda ake zargin da wadanda suka hada baki sunyi kutse cikin gonar ɗauke da muggan makamai wadda hakan na iya janyo tashin hankali.

Ta kuma yi iƙirarin cewa wanda aka yi ƙararsa ya lalata wata mota ƙirar Honda Accord mai lamba L.S.D 655 EV mallakar wani Kazeem Ajiboye.

A cewar mai shigar da ƙarar laifukan sun saba wa sashi na 81, 390(9), 451 da 517 na Criminal Code ta jihar Ogun na shekarar 2006.

Alƙalin da ke shari'ar, Majistare B.S. Abdulsalam ya bada belin wanda aka yi ƙarar a kan kudi 500,000 tare da mutum biyu da za su tsaya masa.

Ya kuma dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 14 ga watan Satumba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel