Kasar UAE ta yaudari duniyar Musulunci yayinda ta hada kai da Isra'ila

Kasar UAE ta yaudari duniyar Musulunci yayinda ta hada kai da Isra'ila

Hadaddiyar daular Larabawa UAE ta yaudari duniyar Muslunci da Falasdinawa ta hanyar shiga sulhu da Isra'ila, Shugaban koli na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana a jawabi.

Falasdinawa sun nuna rashin amincewarsu da hakan saboda zai raunata yarjejeniya da kasashen Larabawa sukayi na yanke alaka da Isra'ila kafin tabbatar da kasar Falasdin.

Falasdinawa sun gudanar da zanga-zanga suna kona tutocin UAE domin nuna fushi, cewar AlJazeera.

"Tabbas, yaudarar UAE ba zai wanye ba, amma ba za'a manta da hakan ba. Sun bari Yahudawa su shiga yankin kuma suka mana da Falasdin," Khamenei ya bayyana ranar Talata.

"Wannan abin kunyan zai cigaba da bin kasar UAE... Ina fatan zasu farka daga baccinsu kuma su gyara abinda sukayi."

Wani jami'in gwamnatin UAE ya yi watsi da jawabin Khamenei.

"Hanyar samar da zaman lafiya da cigaba ba zai yiwu ba ta hanyar zage-zage da kalaman batanci ba," Jami'in ma'aikayar harkokin wajen UAE,"amal Al-Musharakh.

"Ire-iren wadannan kalaman na da barazana ga zaman lafiya a yankin."

Kasar UAE ta yaudari duniyar Musulunci yayinda ta hada kai da Isra'ila
Kasar UAE ta yaudari duniyar Musulunci yayinda ta hada kai da Isra'ila
Source: UGC

Kasar Isra'ila da UAE na sa ran amfana da juna ta fannin tattalin arziki, a wata alakar ta farko irinta tsakanin wata kasar Larabawa da Isara'ila cikin shekaru sama da 20.

Falasdinawa sun bayyana mamaki da bacin ransu kan yadda wannan mataki zai raunata doguwar alaka da kirar da Larabawa ke yiwa Isra'ila su janye daga yankunan Falasdinawa kuma amince da Falasdin a matsayin kasa.

Manyan jami'an kasar UAE sun yi kokarin basar da Falasdinawa ta hanyar cewa sun shiga sulhu da Isara'ila ne saboda ta dakatad da shirin sake kwace filaye a yankin Kudus, kuma Firam Ministan Benjamin Netanyahu ya amince da hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel