Jerin Jihohi 4 da zasu bude jami'o'i da makarantunsu a watan nan

Jerin Jihohi 4 da zasu bude jami'o'i da makarantunsu a watan nan

Bayan watanni biyar da kulle makarantun firamare, sakandare da jami'o'i a fadin Najeriya, da alamun abubuwa zasu dawo yayinda gwamnoni jihohi suka fara sanar da ranakun bude makarantu.

Tuni daliban ajujuwan karshe masu jarabawar WAEC da NECO suka koma makaranta.

Ga jerin jihohi 4 da za'a bude da ranakun:

1. Jihar Kogi

Gwamnatin jihar Kogi a ranar Talata ta sanar da cewa dukkan makarantu mallakin gwamnatin jihar zasu koma aiki ranar 14 ga watan Satumba, 2020.

Kwamishanan ilimin jihar, Mista Wemi jones, ya ce makarantun sun hada da Firamare, Sakandare da na gaba da sakandare.

Ya sanar da hakan ne ranar Talata, 1 ga Satumba, a Lokoja yayin hira da manema labarai

A cewar jones, gwamnatin jihar ta yanke shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

2. Jihar Delta

Jami'o'i a jihar Delta zasu koma bakin aiki ranar 21 ga Satumba, 2020, watanni biyar bayan rufesu domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Majiyoyi daga gwamnatin jihar sun bayyana cewa an yarje da komawan dalibai makarantar ne bayan ganawar gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa da masu ruwa da tsaki.

KU KARANTA: Ku bamu milyan 20 mu saki yaranku: Masu Garkuwa da dalibai a Kaduna sun bukaci kudin fansa

3. Jihar Legas

A ranar 29 ga Agusta, 2020, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bada umurnin bude dukkan jami'o'i mallakan gwamnatin jihar daga ranar 14 ga Satumba, 2020.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai yau Asabar, kamar yadda TheCable ta shaida.

Hakazalika ya bayyana cewa da yiwuwan za'a bude makarantun sakandaren jihar fari daga ranar 21 ga Satumba, 2020.

An rufe makarantun ne a watan Maris sakamakon bullar cutar Korona.

Jihar Legas ke kan gaba wajen yawan adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya.

4. Jihar Osun

Gwamnatin jihar Osun ta sanar da ranar bude makarantun jihar.

Kwamishanar ilimin jihar, Funke Egbemode, ta sanar da hakan ne ranar Litinin inda tace za'a bude ranar 21 ga Satumba, 2020.

A cewarsa, an yanke shawarar haka ne a zaman majalisar zartaswar jihar.

Ta yi kira ga masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa an shirya makaman bude makarantun bisa ka'idojin da ma'aikatar Ilimi ta gindaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel