Hukumar Soji ta mika mutane 778 da ta ceto daga hannun yan ta'addan Darul Salam ga gwamnonin jihohi 16

Hukumar Soji ta mika mutane 778 da ta ceto daga hannun yan ta'addan Darul Salam ga gwamnonin jihohi 16

Hukumar Sojin Najeriya ta mika mutane 778 da aka samu nasarar cetowa daga hannun yan ta'addan Darul Salam ga gwamnatocin asalin jihohinsu 16 da birnin tarayya.

An ceto mutanen ne - yawancinsu mata da yara - sakamakon hadin kan jami'an Soji na musamman dake garin Doma da dakarun Operation Whirl Stroke da suka kai farmaki sansanin yan ta'addan, TVC ta ruwaito.

Darul Salam wata kungiyar yan ta'adda ne da suka addabi yankin Arewa maso tsakiyan Najeriya da wasu jihohin Arewa na tsawon shekaru takwas yanzu.

Hare-haren yan bindiga yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama, garkuwa da mutane, sace-sacen dabbobi a hanyasr Okene-Lokoja da Abaji-Toto.

Sakamakon hakan hukumar Sojin Najeriya tare da na Operation Whirl Stroke suka afka dajin Ugya, dajin Panda, dajin Uttu da tsaunin dake jihar Nasarawa.

KU KARANTA: Ku bamu milyan 20 mu saki yaranku: Masu Garkuwa da dalibai a Kaduna sun bukaci kudin fansa

Hukumar Soji ta mika mutane 778 da ta ceto daga hannun yan ta'addan Darul Salam ga gwamnoni jihohi 16
Hukumar Soji ta mika mutane 778 da ta ceto daga hannun yan ta'addan Darul Salam ga gwamnoni jihohi 16
Asali: Twitter

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa jami’an tsaro sun samu galaba a kan ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan da ake zargi su na yin garkuwa da mutane a titin Abuja zuwa garin Lokoja.

Dakarun bataliya ta 177 na sojojin kasan Najeriya da hadin gwiwar wasu dakaru daga jihar Kogi, da ‘yan banga, sun yi watsa-watsa da sansanin ‘Yan Darusallam.

‘Yan ta’addan Darusallam sun dade su na yin ta’adi a kan iyakokin Kogi da Nasarawa da ke kusa da babban birnin tarayya na kusan tsawon shekaru takwas.

Sansanin Darussalam da ke yankin Ittu ya na kunshe da ‘yan garkuwa da mutane 2000 da miyagun ‘yan bindiga, da kuma ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram.

Rahoton ya ce jami’an sojojin sun kashe wani daga cikin wadanda ake zargin ya na cikin ‘yan bindiga a lokacin da su ke kokarin share dajin da ‘yan ta’addan su ka fake.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng