Jaruma Maryam AB Yola ta fita daga Kannywood, ta daina fim

Jaruma Maryam AB Yola ta fita daga Kannywood, ta daina fim

Jaruma a masana'antar shirya fina finan Hausa, Maryam AB Yola, ta sanar da ficewarta daga fim da kuma ita kanta masana'antar ta Kannywood.

Maryam Yola ta sanar da ficewarta daga masana'antar ne a shafinta na WhatsApp, tana mai cewa, "Assalamu Alaikum, ni Maryam AB Yola ina mai sanar da ku cewa daga yau 1 ga watan Satumba, 2020 na daina fim.

"Haka zalika, na bar Kannywood, kuma ina matukar godiya da kaunan da kuke nuna min. Allah ya sa mu dace ameen."

Sanarwar ficewarta daga fim ya fara fitowa ne daga shafinta na WhatsApp, inda kuma aminiyarta Sayyada Sadiya Haruna ta wallafa hakan a shafinta na Instagram.

Jarumar ta wallafa sanarwar ne da misalin karfe 4:19 na safiyar ranar Talata, inda hukuncin ficewa daga fim zai fara nan take.

KARANTA WANNAN: Surukar Atiku Abubakar kuma matar marigayi Lamido Aliyu Musdafa ta rasu

Ko da wakilin Legit.ng Hausa ya tuntubi Sadiya Haruna kan wannan sanarwa da ta wallafa, ta tabbatar da hakan, inda har ta dauki hoton sanarwar daga shafinta Yola na WhatsApp.

Jaruma Maryam AB Yola ta fita daga Kannywood, ta daina fim
Jaruma Maryam AB Yola ta fita daga Kannywood, ta daina fim
Asali: Twitter

Maryam Abdullahi Bala wanda shine cikakken sunan jarumar, an haife ta ne a ranar 15 ga watan Disambar 1995 a jihar Adamawa.

Sai dai an raine ta a babban birnin tarayya Abuja, bayan da suka koma can da zama da ita da 'yan gidansu gaba daya.

Maryam Yola ta shiga Kannywood a shekarar 2012 inda ta fara fita a fim dinta na farko mai suna Alkawari, da mai bi masa NAS, wanda ta taka rawa tare da jarumi Adam A Zango.

Jaruma Maryam AB Yola ta taba auren fitaccen jarumin Kannywood Adam A Zango, bayan karewar aurensu ne ta dawo Fim a shekarar 2018.

Bayan dawowarta ne ta fara fitowa a bidiyon wakokin Hausa, kamar Salon waka, Muje anfara da sauransu.

Haka zalika ta ci gaba da fim a shekarar ta 2018 zuwa 2020, inda ta fito a fina finai kamar Hafeez, Matar Muce, Yar siyasa, Zainab Ali, Fauwax, Zainul Abideen, Dan Takara da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng