Yadda zamu narka biliyan N600 a bangaren noma - Minista Sabo Nanono

Yadda zamu narka biliyan N600 a bangaren noma - Minista Sabo Nanono

- Sabo Nanono, ministan noma, ya ce gwamnatin tarayya ta yanke shawarar narka biliyan N600 a harkar noma domin farfrado bangaren

- A cewar ministan, tallafin zai hari kananan manoma miliyan 2.4 a rukunin farko

- Ya bayyana cewa domin tabbatar da cewa ba a ci kudin gwamnati a banza ba, tallafin kayan aiki kawai za a bawa manoma banda kudi

Ministan harkokin noma da raya karkara, Sabo Nanono, ya ce gwamnatin tarayya ta yanke shawarar narka biliyan N600 a harkar noma domin farfrado da bangaren.

Nanono, tsohon manomi daga jihar Kano, ya ce za a narkar da kudaden ne a kan kananan manoma domin tabbatar da yalwar abinci da dorewar hakan a fadin kasa.

Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai kamfanin sarrafa takin zamani da hamshakin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya kammala ginawa a jihar Legas.

Kazalika, Nanono ya gana da sauran ma su kamfanonin sarrafa taki da ke Legas domin ganin yadda za a samu hadin kai a tsakaninsu domin tabbatar da yalwar taki a fadin kasa.

Yadda zamu narka biliyan N600 a bangaren noma - Minista Sabo Nanono
Sabo Nanono
Asali: Twitter

Bayanin ministan na kunshe ne a cikin wani jawabi da Theodore Ogaziechi, darektan yada labarai na ma'aikatar noma da raya karkara, ya rabawa manema labarai ranar Lahadi a Abuja.

A cewar Nanono, rabon tallafin biliyan N600 da za a bawa kananan manoma zai fara da manoma miliyan 2.4 a rukuni na farko.

DUBA WANNAN: 2023: Kalu ya ziyarci IBB, ya ce babu tsarin karba-karba a APC

Ministan ya bayyana cewa domin tabbatar da cewa ba a ci kudin gwamnati a banza ba, tallafin kayan aiki kawai za bawa manoma ba kudi ba, kamar yadda aka saba a bay.

Nanono ya kara da cewa rufe iyakokin kasashen duniya da aka yi sakamakon barkewar annobar korona ya nuna cewa Najeriya za ta iya ciyar da kanta ba tare da wani tashin hankali ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel