Batanci ga Annabi: Kungiyar Malaman jihar Kano da kungiyoyin Sakai, sun goyi bayan hukuncin kisan da kotu ta yanke

Batanci ga Annabi: Kungiyar Malaman jihar Kano da kungiyoyin Sakai, sun goyi bayan hukuncin kisan da kotu ta yanke

- Kungiyar Malamai ta jihar Kano tare da hadin guiwar kungiyoyin sakai na jihar sun goyi bayan hukuncin kisan da kotu ta yanke

- A kwanakin baya ne dai kotun shari'a ta jihar Kano ta yankewa saurayin hukuncin kisa bayan kama shi da laifin zagin Annabi

Kungiyar Malaman jihar Kano da kungiyoyin sakai na (NGO) na jihar Kano sun nuna goyon bayansu dari bisa dari akan hukuncin kisan da aka yankewa mawakin da yayi batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Wannan ya fito ne ta wata sanarwa da shugaban kungiyar hadin guiwar, Farfesa Musa Muhammad Borodo, wanda yace kama mawakin da kuma hukuncin da aka yanke masa shine ya kawo karshen wannan lamari.

Batanci ga Annabi: Kungiyar Malaman jihar Kano da kungiyoyin Sakai, sun goyi bayan hukuncin kisan da kotu ta yanke
Batanci ga Annabi: Kungiyar Malaman jihar Kano da kungiyoyin Sakai, sun goyi bayan hukuncin kisan da kotu ta yanke
Source: Facebook

Ya kara da cewa kungiyar bata ji dadin martani da kungiyoyi da masu kare hakkin dan adam suke yi ba, ba tare da duba ga laifin da wanda yayi laifin yayi ba da kuma yankin da mutumin yayi laifin.

Haka kuma sanarwar ta yabawa gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, akan goyon baya da ya nuna da kuma girmama hukuncin kotu tare da kawo mutanen da yake mulka a farko kafin komai.

Idan ba a manta ba, kotun Shari'a ta jihar Kano ta yankewa Yahaya Sharif-Aminu, matashi mai shekaru 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an same shi da laifin yin batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

KU KARANTA: Barayi sun sace mai jego kwana hudu bayan ta haihu a jihar Taraba

A wani rahoto makamancin haka kuma, LEGIT ta kawo muku rahoton wasu mutum biyu daga cikin mabiyan Sheikh Ibrahim Zakzaky, da suka rasa ransu sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin jami'an 'yan sanda da su a Kaduna a jiya Lahadi.

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa an jiyo harbin bindiga akan babbar hanyar Ahmadu Bello Waya a jiya da rana, a lokacin da 'yan sandan suke kokarin tarwatsa dandazon 'yan shi'ar.

'Yan Shi'ar dai sun fito zanga-zanga ne domin kara nuna bukatarsu ta a sakar musu shugaban su Sheikh Ibrahim Zakzaky, da matarsa, Zeenat, wadanda ake tsare dasu tun a watan Disambar shekarar 2015, sakamakon rikicin da suka yi da jami'an hukumar soji a Zaria.

Sai dai kuma, tuni gwamnatin jihar Kaduna ta riga ta haramta wannan kungiya ta kuma hana duk wata zanga-zanga da kungiyar za ta yi a jihar. An kashe mutum 2, da yawa sun jikkata yayin wani rikici da ya barke tsakanin 'yan Shi'a da 'yan sanda a Kaduna

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel