An bindige jigon jam'iyyar PDP a yayin da yake dawowa daga wajen taron jam'iyya

An bindige jigon jam'iyyar PDP a yayin da yake dawowa daga wajen taron jam'iyya

- Jigo kuma kansila a jam'iyyar PDP Karma Agagowei, ya mutu sakamakon harbin shi da 'yan bindiga suka yi a jihar Bayelsa

- Kafin ya mutu dai Agagowei shine kansilan dake wakilatr Ward 6 dake karamar hukumar Sagbama cikin jihar ta Bayelsa

- 'Yan bindiga ne suka kaiwa jigon jam'iyyar PDP din a daidai lokacin da yake kan hanyar shi ta dawowa daga wajen taron jam'iyya a ranar Asabar da daddare

'Yan bindiga sun kashe kansilan dake wakiltar Ward 6 dake cikin karamar hukumar Sagbama cikin jihar Bayelsa mai suna Mr Karma Agagowei.

An ruwaito cewa an harbe Agagowei a yankin Opolo dake Yenagoa, babban birnin jihar, a lokacin da yake kan hanyarshi ta dawowa daga taron jam'iyyar PDP da aka gabatar a ranar Asabar.

An bindige jigon jam'iyyar PDP a yayin da yake dawowa daga wajen taron jam'iyya
An bindige jigon jam'iyyar PDP a yayin da yake dawowa daga wajen taron jam'iyya
Source: UGC

Anyi gaggawar garzayawa da shi zuwa asibiti a cikin garin Yenagoa, amma ba ayi masa magani ba saboda rashin rahoto daga wajen 'yan sanda.

An ruwaito cewa ya mutu jim kadan bayan kai shi asibitin.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: 'Yan Boko Haram sun kashe mutane 14 akan iyakar Najeriya da Kamaru

Haka kuma an ruwaito cewa, wani mutumi da suka shigo Keke-Napep daya da kansilan a lokacin da lamarin ya faru, shima an sare shi da adda. Amma ya rayu sai dai ya samu raunika da yawa.

Marigayi Agagowei yana daya daga cikin kansiloli 105, wadanda aka zaba a lokacin da aka gabatar da zaben kananan hukumomi na jihar a watan Agustan shekarar 2019.

Da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Mr Asinim Butswat, ya ce yana jiran rahoto akan lamarin shi ma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel