Mali: An cimma matsaya tsakanin sojojin juyin mulki da ECOWAS

Mali: An cimma matsaya tsakanin sojojin juyin mulki da ECOWAS

Kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, ta ce sojojin juyin mulki na kasar Mali sun amince da mika mulki nan da shekara daya cif.

An yi wannan yarjejeniyar ne wacce kuma aka bai wa manema labarai a ranar Asabar, bayan gagarumin taron da aka yi da shugabannin kasashe, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da masu juyin mulkin, ta yanar gizo.

Taron ya duba rahoton kungiyar sasanci ta ECOWAS wacce ta kai ziyara tsakanin 22 ga watan Augustan 2020 zuwa 24 ga watan Augustan, don duba ci gaban kwanan nan a Mali.

Ta yi kira ga dakarun sojin Malin da su gaggauta fara shirin mika mulki ga farar hulan, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada da kuma jam'iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki.

ECOWAS ta yi kira garesu da su gaggauta zaben shugaban kasar na sauyin mulki, jaridar The Punch ta bayyana.

Takardar ta ce, "Dole ne shugaban ya kasance farar hula kuma sannannen mutum mai nagartattun halayya, kwazo da kuma dabi'a wanda zai rike mulkin.

"Shugaban rikon kwaryar ba zai iya tsayawa takarar zaben shugaban kasa mai zuwa ba."

Taron ya kara da duba hukuncin shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita wanda ya yi murabus da kuma sakin sauran jami'an gwamnati da aka kame.

Mali: An cimma matsaya tsakanin sojojin juyin mulki da ECOWAS
Mali: An cimma matsaya tsakanin sojojin juyin mulki da ECOWAS. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa

A wani labari na daban, skasashe da gwamnatocin kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen Afrika ta kudu (ECOWAS), za su shiga ganawa ta musamman a kan halin da siyasar kasar Mali take ciki.

Daraktan fannin yada labarai na ECOWAS ne ya sanar da hakan a garin Abuja a ranar Laraba.

An kira ganawar ta gaggawa wacce za a yi ta yanar gizo, sakamakon juyin mulkin da dakarun sojin kasar Mali suka yi a ranar Talata.

Sojin hamayya sun damke shugaban kasar Mali, Boubacar Keita tare da Firayim minista Boubou Cisse a ranar Talata, inda suka tafi da su wata babbar barikin sojoji da ke wajen babban birnin jihar na Bamako.

Daga bisani, shugaban kasa Keita ya snaar da yin murabus dinsa don gujewa zubar da jini. Da gaggawwa ECOWAS ta yi martani inda ta dauka alkawarin rufe dukkan iyakokin kasashen da ke karkashinta da kasar Mali, sannan kasar za ta fuskanci ladabtarwa bayan dakatar da ita da aka yi daga kungiyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel