Gwamnatin Kaduna ta hana masu adaidaita sahu aiki a manyan tituna

Gwamnatin Kaduna ta hana masu adaidaita sahu aiki a manyan tituna

- Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana sabon tsarin sufurinta inda ta haramta wa masu adaidaita sahu hawa kan manyan tituna

- Ana tsammanin hukumar tabbatar da dokokoin kan tituna ta jihar Kaduna (KASTLEA), za ta tabbatar da bin sabuwar dokar

- Kamar yadda darakta janar ta hukumar sufuri ta jihar Kaduna, Aisha Sa'idu Bala, ta bayyana, hakan zai rage cunkoso a titunan jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta wa masu adaidaita sahu ko kuma Keke Napep daga hawa manyan titunan babban birnin, kamar yadda sabbin tsare-tsaren fannin sufuri ya tanadar.

Babbar hanyar Kawo zuwa titin Ali Akilu zuwa hanyar Ahmadu Bello, suna daga cikin inda aka haramta wa adaidaita sahun bi. Dokar za ta fara daga ranar 31 ga watan Augustan 2020.

Hukumar tabbatar da dokokin kan titi na jihar Kaduna (KASTLEA), za ta tabbata da wannan haramcin, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Aisha Sa'idu Bala, darakta janar ta hukumar sufuri ta jihar Kaduna,ta ce jihar ta habaka sabbin dokokin don masu ababen hawa na haya a jihar.

Ta ce an samar da wani sabon tsari na ware hanyoyi da kuma lasisi ga masu adaidaita sahun don bai wa matukan motocin haya da adaidaita sahun jihar sabon fasali.

"An yi hakan ne don daidaitawa tare da habaka tsari ga masu ababen hawa na haya. Hakan zai taimaka wurin rage cunkoso tare da daidaituwa ga fasinjoji," tace.

Gwamnatin Kaduna ta hana masu adaidaita sahu aiki a manyan tituna
Gwamnatin Kaduna ta hana masu adaidaita sahu aiki a manyan tituna. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda wani mutum ya riƙa kuka yana birgima cikin taɓo don budurwarsa ta ƙi yarda ta aure shi

Darakta janar din ta ce, hukumar ta fara rijista ga masu adaidaita sahun a watan Yuli, kuma za ta kare a watan Satumba.

A wani labari na daban, wasu mutane da ake zargin yan bindiga ne sun yi awon gaba da jami'in dan sanda, jami'in hukumar Sibil Defens NSCDC, wata yarinya da wani mutum a jihar Kaduna.

An dauke jami'an tsaron biyu ne a gidajensu dake unguwar Maraban Rido, karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna a daren Alhamis, 27 ga Agusta, 2020.

Yan bindigan sun kai hari unguwar ne cikin dare misalin karfe 12 inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi kafin suka yi awon gaba da su.

Duk da cewa hukumar yan sanda bata tabbatar da dauke jami'inta ba har yanzu, kakakin hukumar NSCDC na jihar Kaduna, Orndiir Terzungwe, ya tabbatarwa Channels TV labarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel