Idan dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa a 2023 za a ga canji - Ohanaeze Ndigbo

Idan dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa a 2023 za a ga canji - Ohanaeze Ndigbo

Kungiyar yan kabilar Igbo a Najeriya, Ohanaeze Ndigbo, ta ce idan Najeriya ta samu shugaban kasa Igbo a shekarar 2023, za a ga sauyi a kasar, TheCable ta ruwaito.

Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Nnia Nwodo, ya bayyana hakan ne a sakon murnar da ya aikawa dan Najeriya, Kelechi Madu, wanda aka nada Ministan Shari'a a kasar Canada.

Kelechi Madu shine dan Afrika na farko da ya taba hawa kujerar Ministan Shari'a a kasar Canada.

A sakon taya murnan da mai magana da yawun Nwodo, Emeka Attamah, ya rattafa hannu, ya jinjinawa Madu bisa wannan cigaba da ya samu.

Ya ce kungiyar Ohanaeze Ndigbo na alfahari da Kelechi Madu, kuma idan aka zabi shugaban kasa Igbo a 2023, zai kawo sauyi Najeriya.

Nwodo ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta daina nuna wariya da Inyamurai saboda akwai alfamu da dama tattare da su.

Yace: "Gwamnatin tarayya ta daina nuna wariya da cin mutuncin Igbo a kasar nan saboda a ribaci ilmomi da basiranmu domin amfanin kasa gaba daya."

"Najeriya za ta ga kyakkyawan sauyi idan dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa a 2023."

Idan dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa a 2023 za a ga canji - Ohanaeze Ndigbo
Idan dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa a 2023 za a ga canji - Ohanaeze Ndigbo
Source: Facebook

KU KARANTA: Batanci ga Annabi a Kano: Lauyoyi na tsoron taimakawa Yahaya Sharif-Aminu

A bangare guda, Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Okwesilieze Nwodo, ya ce idan ba'a baiwa kabilar Igbo shugabancin kasa a 2023 ba, masu arzikin kudu maso yamma zasu hada kai da shugaban kungiyar yakin neman Biyafara IPOB, Nnamdi Kanu wajen ballewa daga Najeriya.

Nnamdi Kanu ya kasance kan gaba wajen yakin neman yancin yankin kabilar Igbo saboda yadda aka mayar da yan yankin saniyar ware.

Ya tsere daga Najeriya bayan samun beli daga kotu.

A hirar Okwesilieze Nwodo da jaridar Vanguard, ya jinjinawa Tanko Yakassai, bisa kiran da yayi a baiwa Igbo shugabancin kasa a 2023.

Ya ce shekaru 50 kenan ana cin zarafin Igbo, kuma ya shawarci dukkan masu son rana goben yaransu yayi kyau su zabi Igbo a 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel