Gobara ta lashe gini mai hawa daya a Legas

Gobara ta lashe gini mai hawa daya a Legas

Gobara ta lashe wani gini mai hawa ɗaya da ke gida mai lamba 10 Moliki Street a ƙaramar hukumar Mushin a jihar Legas.

An ruwaito cewa gobarar da ta fara ci misalin ƙarfe 8 na safe a cinye benen na farko baki ɗaya.

Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Legas, Nosa Okunbor ya tabbatar wa wakilin The Punch afkuwar lamarin a wayar tarho.

Da duminsa: Gobara ta lashe wani bene a Legas
Da duminsa: Gobara ta lashe wani bene a Legas. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

Ya ce kawo yanzu ba a gano abinda ya yi sanadin gobarar ba amma ana nan ana ƙoƙarin ceto mutane da duniyoyi a wurin.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Jirgi mai saukar ungulu ya afka wa wani gini a Legas

A wani rahoton daban, kun ji cewa wani jirgi mai saukan ungulu ya yi hatsari a jihar ta Legas a ranar Juma'a 29 ga watan Agustan 2020 a Salvation Road, Opebi, Ikeja.

Lamarin mai tayar da hankali ya yi sanadin rasa rayuka uku na wadanda ke cikin jirgin bayan jirgin ya faɗa kan wata katanga da ta raba wasu gidaje biyu a 16A, Salvation Road.

Ga dai wasu muhimman abubuwa 5 da ya dace ku sani game da hadarin kamar yadda The Nation ta tattaro:

1. Jirgin mai saukan ungulu, Bell 206-3 mai lambar rajista 5N-BQW mallakar Quorum Aviation ne.

2. Jirgin mallakar kamfanin sufurin ya taso ne daga Fatakwal, babban birnin jihar Rivers ɗauke da matuƙa biyu da fasinja guda ɗaya.

3. Saura kimanin mintuna biyu jirgin ya isa wurin da za shi wato filin tashin jirage na Murtala Muhammed da ke Ikeja, Legas.

4. Matuƙan jirgin biyu sun mutu nan take, shi kuma mutum na uku a jirgin ya mutu daga baya a asibitin koyarwa da jami'ar Legas da ke Ikeja.

5. Cikin ikon Allah, jirgin bai yi sanadin mutuwar kowa ba a gidajen da ya faɗa bayan ya yi haɗarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel